Abdoul Kairou Amoustapha (an haife shi a ranar 1 ga watan Janairu, shekara ta 2001) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Nijar wanda a halin yanzu yake bugawa Cancún wasa a gasar La Liga de Expansión MX. [1]

Kairou Amoustapha
Rayuwa
Haihuwa Niamey, 1 ga Janairu, 2001 (24 shekaru)
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
 

Amoustapha ya koma ASN Nigelec zuwa Loudoun United a gasar USL a ranar 20 ga watan Fabrairu shekara ta 2020. Ya fara wasansa na farko a ranar 2 ga watan Agusta shekarar 2020, yana farawa da Hartford Athletic a cikin rashin nasara 1 zuwa 4.

A watan Oktoba shekara ta 2020, Amostapha ya fara horo tare da ƙungiyar iyayen Loudoun DC United bayan kammala kakar Loudoun. A cikin watan Oktoba shekarar 2021, an sake kiran Amoustapha zuwa kulob ɗin iyayensa, MFK Vyskov. Daga baya an aika shi zuwa Cancún FC nan da nan bayan dawowarsa daga Loudoun. [2]

Ƙasashen Duniya

gyara sashe

Amoustapha ya buga wasanni uku kowacce a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Niger U-17 da U-20. Ya ci ƙwallon sa na farko ta ƙasa da ƙasa tare da tawagar 'yan ƙasa da shekaru 20 a gasar cin kofin Afrika na 'yan ƙasa da shekaru 20, a ranar 9 ga watan Fabrairu, shekara ta 2019, a kan 'yan wasan Burundi na 'yan ƙasa da shekaru 20, a wasan da suka tashi 3-3. season.[3]

A ranar 31 ga watan Oktoba, shekara ta 2020, babbar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Niger ta kira Amoustapha a matsayin wani bangare na tawagar share fagen shiga gasar cin kofin kasashen Afrika na shekarar 2021. Daga baya ya buga wasansa na farko tare da tawagar ƙasar a ranar 13 ga watan Nuwamba, inda ya shigo a matsayin wanda zai maye gurbinsa a wasan da Nijar ta doke Ethiopia da ci 1-0. [4]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Loudoun United FC have acquired Abdoul Kairou Amoustapha and Massimo Ferrin". Loudoun United FC. February 20, 2020. Archived from the original on January 18, 2022. Retrieved May 16, 2022.
  2. "Hartford Athletic vs. Loudoun United FC - August 2, 2020 | USLChampionship.com". www.uslchampionship.com.
  3. Keefer, Ryan (2020-10-19). "Kairou Amoustapha proving to be worth the wait for Loudoun". Black And Red United (in Turanci). Retrieved 2020-10-19.
  4. Staff (2021-10-05). "Loudoun United FC Announce that Midfielder Kairou Amoustapha Has Been Recalled to his Parent Club, MFK Vyskov". Loudoun United FC (in Turanci). Archived from the original on 2022-01-13. Retrieved 2022-01-13.