Juma Kapuya
Juma Athumani Kapuya (an haife shi ranar 22 ga watan Yuni, 1945) ɗan siyasan Tanzaniya ne na CCM kuma ɗan Majalisar Tarayya a mazabar Urambo ta Yamma tun shekara ta 1995.
Juma Kapuya | |||||
---|---|---|---|---|---|
4 ga Janairu, 2006 - 20 ga Janairu, 2014 - Hussein Mwinyi (en) →
| |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Tanganyika Territory (en) , 22 ga Yuni, 1945 (79 shekaru) | ||||
ƙasa | Tanzaniya | ||||
Harshen uwa | Harshen Swahili | ||||
Karatu | |||||
Makaranta |
Jami'ar Dar es Salaam Aberystwyth University (en) | ||||
Harsuna |
Turanci Harshen Swahili | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||
Employers | Jami'ar Dar es Salaam | ||||
Imani | |||||
Jam'iyar siyasa | Party of the Revolution (en) |
Ayyuka
gyara sasheKapuya ya kasance memba na Majalisar Zartarwa ta kasa ta Chama Cha Mapinduzi (CCM) daga shekara ta 1997 zuwa shekara ta 2005. Bayan ya zama Ministan kwadago, ci gaban matasa da wasanni, an nada Kapuya a matsayin Ministan Tsaro da Bautar Kasa a ranar 4 ga watan Janairun shekara ta 2006. [1] Bayan shekaru biyu a matsayin Ministan Tsaro, an nada shi Ministan kwadago, Aiki da Ci gaban Matasa a ranar 12 ga watan Fabrairun, shekara ta 2008. [2]
Shi dan majalisar CCM ne a Majalisar Dokokin Tanzania, yana wakiltar mazabar Urambo West. Kafin aikinsa na gwamnati, Kapuya farfesa ne a fannin ilimin tsirrai a Jami'ar Dar es Salaam .
Manazarta
gyara sashe- ↑ Hassan Muhiddin, "JK’s beefed up team", Guardian (IPP Media), January 5, 2006.
- ↑ Austin Beyadi, "Public welcomes new cabinet", Guardian (IPP Media), February 13, 2008.