Julian Brandt ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Jamus wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan gefe ko kuma na tsakiya mai kai hari ga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Borussia Dortmund da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta kasa ta Jamus.[1]

Julian Brandt
Rayuwa
Haihuwa Bremen, 2 Mayu 1996 (28 shekaru)
ƙasa Jamus
Harshen uwa Jamusanci
Karatu
Harsuna Jamusanci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Germany national under-15 football team (en) Fassara2011-201122
  Germany national under-16 football team (en) Fassara2011-201231
  Germany national under-17 association football team (en) Fassara2012-2013195
  Germany national under-19 football team (en) Fassara2013-2014122
Bayer 04 Leverkusen (en) Fassara2014-201916534
Bayer 04 Leverkusen II (en) Fassara2014-201411
  Germany national under-21 football team (en) Fassara2015-201681
  Germany national under-20 football team (en) Fassara2015-201562
Germany national under-23 football team (en) Fassara2016-201660
  Germany national association football team (en) Fassara2016-unknown value473
  Borussia Dortmund (en) Fassara2019-unknown value15630
 
Muƙami ko ƙwarewa wing half (en) Fassara
attacking midfielder (en) Fassara
Lamban wasa 19
Nauyi 82 kg
Tsayi 185 cm

Brandt ya buga wasanni sama da 55 a jumulla da kungiyoyin matasan Jamus, yana wasa a kowane mataki daga U15 zuwa U21.[2] Ya kasance memba a cikin tawagar da ta lashe gasar cin kofin nahiyar Turai ta 'yan kasa da shekaru 19 a 2014.[3][4]

Sana'ar Kungiya gyara sashe

Julian Brandt an haife shi kuma ya girma a Bremen. A lokacin matashi, ya taka leda a garinsu a kungiyar SC Borgfeld sannan a kungiyar FC Oberneuland kafin ya shiga makarantar matasa ta (Nachwuchsleistungszentrum) ta kungiyar kwallon kafa ta VfL Wolfsburg.

Sana'ar Kasa gyara sashe

A ranar 17 ga watan Mayu a shekarar 2016, an saka sunan Brandt a cikin tawagar farko na mutum 27 na Jamus don zuwa gasar cin kofin kasashen turai Yuro 2016. Ya kasance cikin 'yan wasan da za su taka leda a gasar Olympics ta bazara ta 2016, inda Jamus ta lashe lambar azurfa.

A ranar 4 ga Yuni 2018, an haɗa Brandt cikin tawagar mutane 23 na ƙarshe na Jamus don gasar cin kofin duniya ta FIFA na 2018.A ranar 17 ga watan Yuni, Brandt ya fara fitowa gasar cin kofin duniya a matsayin wanda zai maye gurbin Timo Werner a minti na 86 a wasan farko da Mexico inda suka sha kashi da ci 1-0.

Manazarta gyara sashe