Joye Estazie (an haife shi ranar 10, ga watan Agusta 1984) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Mauritius wanda a halin yanzu yake taka leda a matsayin mai tsaron baya ga kungiyar kwallon kafa ta AS de Vacoas-Phoenix a cikin Mauritius League.

Joye Estazie
Rayuwa
Haihuwa Moris, 10 ga Augusta, 1984 (40 shekaru)
ƙasa Moris
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Mauritius men's national football team (en) Fassara2010-
AS de Vacoas-Phoenix (en) Fassara2011-
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga baya

Estazie ya fara aikinsa na ƙwararru a cikin shekarar 2006 tare da kungiyar kwallon kafa ta PAS Mates na Mauritian League, inda daga baya ya zama kyaftin na ƙungiyar. A shekarar 2011, ya koma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta AS de Vacoas-Phoenix.

Ayyukan kasa da kasa

gyara sashe

Estazie ya ci wa Mauritius wasa takwas. A ranar 9 ga watan Oktoba, 2010, ya ci wa Senegal kwallon da kansa a minti na 90 na wasan share fagen shiga gasar AFCON na Mauritius, inda Mauritius ta sha kashi da ci 7-0.[1] Ya zura kwallonsa ta farko a Mauritius a wasan sada zumunci da suka yi da Réunion a watan Satumban 2012. [2]

Manazarta

gyara sashe
  1. Estazie Own Goal Archived 2010-11-14 at the Wayback Machine
  2. Match Report vs Reunion