Josephine Orji (an haife ta a ranar 8 ga watan Afrilu, 1979) ƙwararriyar 'yar wasan powerlifter ce kuma 'yar Najeriya ce.

Josephine Orji
Rayuwa
Haihuwa 8 ga Afirilu, 1979 (45 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a weightlifter (en) Fassara

A ranar 14 ga watan Satumbar a shekarar 2016, ta lashe zinari a matakin mata na +86kg a gasar wasannin nakasassu ta bazara ta shekarar 2016 a Brazil kafin ta ci gaba da kafa sabon tarihin duniya da wasanni ta hanyar daga 160kg a daidai wannan taron.[1][2]

Sana'a/Aiki gyara sashe

Josephine ta sami sha'awar motsa jiki a cikin shekarar 2001 bayan ta ziyarci gidan motsa jiki a Owerri kuma ta gwada wasanni a karon farko. Bayan haka, ta bar aikinta na ƙwararriyar kwamfuta a wani gidan cin abinci na Intanet kuma ta fara horar da ita don haɓaka sana'ar motsa jiki a matsayin mai ɗaukar karfi (Powerlifter).[3]

Manazarta gyara sashe

  1. Duro Ikhazuagbe (15 September 2016). "Nigeria's Josephine Orji Shatters World Record at Rio Paralympics". ThisDay News. Retrieved 18 September 2016.
  2. "Paralympic: Josephine Orji breaks new records, wins gold". Vanguard Newspaper. 14 September 2016. Retrieved 18 September 2016.
  3. Orji on the highs and lows of a Paralympic champion". BBC Sport. Retrieved 13 October 2020.