Joseph Amoako (an haife shi a ranar 13 ga watan Satumba Shekarar 2002) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Ghana wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan tsakiya a ƙungiyar Helsingborgs ta Sweden IF . A baya ya buga wasa a kungiyar Asante Kotoko ta Ghana .

Joseph Amoako
Rayuwa
Haihuwa Ghana, 13 Satumba 2002 (22 shekaru)
ƙasa Ghana
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
 

Amoako ya fara aikinsa ne da kulob din Young Red Bull na yankin Tsakiya, wanda ke mataki na kasa a gasar rukuni na biyu. A watan Oktoba shekarar 2021, Amoako ya koma kungiyar Asante Kotoko a gasar Premier ta Ghana kan kwantiragin shekaru uku yana ci gaba da zama a kungiyar har zuwa shekarar 2024. [1]

A cikin watan Fabrairu shekarar 2022, ya shiga Helsingborgs IF akan yarjejeniyar lamuni ta farko ta shekara guda tare da zaɓi don sanya ta dindindin. A ranar 14 ga watan Fabrairu shekarar 2022, ya buga wasansa na farko a kulob din bayan ya fito a cikin mintuna na 78 a wasan sada zumunci da kungiyar FC Nordsjaelland ta Danish wanda ya kare da ci 4–2 a hannun Helsingborgs IF.

Manazarta

gyara sashe
  1. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named :0

Hanyoyin haɗi na waje

gyara sashe
  • Joseph Amoako at Global Sports Archive
  • Joseph Amoako at Soccerway

Samfuri:Helsingborgs IF squad