Babatunde Joseph Adeyemi[1] Bishop ne na Anglican[2] a kasar Najeriya, [3] shi ne Bishop na Badagry a halin yanzu.[4]

An haifi Adeyemi a ranar sha hudu 14 ga watan Janairun shekara ta alif dubu daya da dari tara da hamsin da bakwai wato 1957 a Ojo, Jihar Legas . Ya yi karatu a Kwalejin Horar da Malaman Gwamnati, Badagry; Kwalejin tauhidin Immanuel, Ibadan; da Jami'ar Jihar Legas. Bayan shekaru uku a matsayin malami, An nada shi dikon a 1984 kuma firist a alif dubu daya da dari tara da tamanin da shida 1986. Bayan ya yi aiki a Ebute Metta ya yi aiki ne a Awodi-Ora, Idumu da Festac Town. Ya zama Canon a 1999 kuma Archdeacon na Festac a 2000.

An tsarkakewa shi a matsayin Bishop na farko na Badagry a ranar sha uku ga Maris shekarar dubu biyu da biyar 2005. [2] Ya kasance mai kula da kungiyar Legas Scripture Union tun shekara ta 2010.

  1. Anglican Communion Office. "Diocese - Nigeria - Badagry". anglicancommunion.org. Retrieved 2020-12-04.
  2. "Church of Nigeria now has 91 dioceses". www.anglicannews.org. Retrieved 2021-03-14.