Jonas Junias Jonas (an haife shi a ranar 24 ga watan Nuwamban 1993 a Swakopmund) ƙwararren ɗan damben Namibiya ne kuma ɗan takara a Gasar Olympics ta bazarar shekarar 2016.[1][2]

Jonas Jonas
mutum
Bayanai
Jinsi namiji
Ƙasar asali Namibiya
Suna Jonas
Sunan dangi Jonas
Shekarun haihuwa 24 Nuwamba, 1993
Wurin haihuwa Swakopmund (en) Fassara
Sana'a boxer (en) Fassara
Wasa boxing (en) Fassara
Participant in (en) Fassara boxing at the 2016 Summer Olympics – men's light welterweight (en) Fassara da boxing at the 2020 Summer Olympics – men's lightweight (en) Fassara

Jonas ya halarci makarantar firamare ta Vrederede, makarantar sakandare ta Atlantic Junior da SI Gobs Secondary School, ya sami suna a cikin shekarar 2014, lokacin da ya ci lambar azurfa a gasar Commonwealth yana da shekaru 20. Ana cikin haka ne ya zama ɗan damben boksin Namibia na huɗu da ya lashe lambar yabo a gasar Commonwealth.

Ya yi takara a ajin mara nauyi na maza a gasar Olympics ta bazara shekarar 2016 a Rio de Janeiro. Hassan Amzile na Faransa ya doke shi a zagaye na 32.[3] Ya kasance mai ba da tuta ga Namibiya a lokacin faretin al'ummai.[4]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-03-30. Retrieved 2023-03-30.
  2. https://web.archive.org/web/20160806061930/https://www.rio2016.com/en/athlete/jonas-junias-jonas
  3. https://web.archive.org/web/20160902095710/https://www.rio2016.com/en/boxing-standings-bx-mens-light-welter-64kg
  4. https://olympics.com/en/news/the-flagbearers-for-the-rio-2016-opening-ceremony