Johnston Busingye
Johnston Busingye lauya ne dan kasar Rwanda, hakazalika shine Babban Kwamishinan Ruwanda a Burtaniya na yanzu. [1] A baya, ya yi aiki a matsayin Ministan Shari'a kuma Babban Lauyan Gwamnati, daga shekarar 2013 zuwa 2022. [2]
Johnston Busingye | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Uganda, |
ƙasa | Ruwanda |
Mazauni | Kigali |
Karatu | |
Makaranta |
John F. Kennedy School of Government (en) Jami'ar Makerere |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Farkon rayuwa da ilimi
gyara sasheYana da digiri na farko a fannin shari'a, wanda ya samu a jami'ar Makerere . Har ila yau, yana da Difloma a fannin Ayyukan Shari'a, wanda Cibiyar Bunkasa Shari'a a birnin Kampala ta ba shi.
Sana'a
gyara sasheJohnston Busingye ya rike mukamai da dama a gwamnatin Rwanda da kuma a bangaren shari'a na kasar Rwanda. daga 2006 zuwa 2013, ya zama shugaban babbar kotun kasar Rwanda. Sauran ayyukan da ya yi a baya, sun haɗa da matsayin mai gabatar da ƙara na ƙasar Rwanda, a matsayin babban sakatare a ma'aikatar shari'a (Minijust), da kuma matsayin babban alkali na kotun shari'a ta gabashin Afirka (EACJ).[ana buƙatar hujja] A matsayinsa na Ministan Shari'a, ya sanar a watan Yuli 2014, shawarar da gwamnatin Rwanda ta yanke, ba zai zama memba naa Kotun Hukunta Manyan Laifuka (ICC) ba.[3]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "High Commissioner Johnston Busingye presents his credentials to Her Majesty Queen Elizabeth II". www.rwandainuk.gov.rw (in Turanci). Retrieved 2022-11-27.
- ↑ Minijust (7 August 2017). "Busingye Johnston is the Minister of Justice and Attorney General of the Republic of Rwanda". Rwanda Ministry of Justice (Minijust). Archived from the original on 7 August 2017. Retrieved 7 August 2017.
- ↑ Mugabe, Robert (31 July 2014). "Rwanda will not join Rome statute—Justice Minister". Great Lakes Voice. Retrieved 7 September 2017.