John Wash Pam John Wash Pam (22 Oktoba 1940 – 1 ga Mayu 2014) ɗan siyasan Najeriya ne wanda ya kasance Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya daga shekarar 1979 zuwa 1983. An zabe shi a matsayin dan majalisar dattawa a karkashin Jam’iyyar Jama’ar Najeriya ta Dr Nnamdi Azikiwe [NPP]. An zabe shi mataimakin shugaban majalisar dattijai ne a bisa yarjejeniyar da aka kulla tsakanin jam’iyyarsa da kuma jam’iyyar NPN mai mulkin kasar. An kira yarjejeniyar "Yarjejeniyar NPN/NPP". Ya rasu ne a shekarar 2014 daga cutar kansar prostate Sen JOHN WASH PAM wanda ya fito daga karkarar rahwol fwi, ron Foron dake karamar hukumar BARKIN LADI ta jihar Filato.

John Wash Pam
Deputy President of the Nigerian Senate (en) Fassara

1979 - 1983
Rayuwa
Haihuwa 22 Oktoba 1940
ƙasa Najeriya
Mutuwa 1 Mayu 2014
Yanayin mutuwa Sababi na ainihi (Ciwon daji na prostate)
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Manazarta

gyara sashe