John Mabuku

Ɗan siyasar Namibia

John Mabuku, (ya mutu 13 ga watan Yuli, 2008). shi ne gwamnan yankin Caprivi a Namibiya kuma mai goyon bayan ɓallewar yankin Caprivi mai cin gashin kansa. Mabuku, wanda tsohon memba ne na Democratic Turnhalle Alliance National Council, ya gudu zuwa gudun hijira a Botswana tare da tsohon shugaban DTA Mishake Muyongo sakamakon rashin nasarar tawayen ƴan Arewa a shekara ta 1998, a yankin Caprivi da gwamnatin Namibiya.[1]

John Mabuku
Rayuwa
Haihuwa 20 century
ƙasa Namibiya
Mutuwa 13 ga Yuli, 2008
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Wurin aiki Katima Mulilo (en) Fassara
Imani
Jam'iyar siyasa Democratic Turnhalle Alliance (en) Fassara

Mabuku ya ci gaba da dai-dai-ta ayyukan DTA daga sansanin 'yan gudun hijira na Kagisong a Botswana kuma ya ci gaba da tallafawa shugaban DTA Mishake Muyongo, wanda ke gudun hijira a Denmark. Ya rasu a gudun hijira a Botswana a ranar 13 ga watan Yuli 2008, bayan ya yi fama da rashin lafiya.[1]

Duba kuma

gyara sashe
  • Caprivi rikici
  • Caprivi na cin amanar kasa

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 "Mabuku Dies in Exile". The Namibian. 2008-07-16. Retrieved 2008-02-24.