João Baptista Borges (an haife shi 4 Janairu 1964, Luanda) masani ne a fannin ilimi kuma ɗan siyasa ne na ƙasar Angola wanda ya yi aiki a matsayin Ministan Makamashi da Ruwa a ƙarƙashin Shugaba José Eduardo dos Santos da João Lourenço daga shekara ta 2012 zuwa yau.[1] Farfesa ne a fannin Injiniyanci a Jami'ar Agostinho Neto kuma memba ne a ofishin siyasa na MPLA.[2] Yana magana da harsunan ƙasashen waje guda uku, Ingilishi, Faransanci da Sipaniyanci sosai.

João Baptista Borges
Minister of Energy and Water (en) Fassara

26 Satumba 2017 -
Minister of Energy and Water (en) Fassara

26 Satumba 2012 - 26 Satumba 2017
Rayuwa
Haihuwa 4 ga Janairu, 1964 (60 shekaru)
ƙasa Brazil
Karatu
Makaranta University of São Paulo (en) Fassara
Harsuna Portuguese language
Sana'a
Sana'a anthropologist (en) Fassara da ɗan siyasa
Employers University of São Paulo (en) Fassara

Faransanci, Turanci, Sipaniyanci.

Ilimi gyara sashe

Borges ya yi karatun digiri na farko a Injiniyan Lantarki a Jami'ar Agostinho Neto a shekara ta 1991, sannan ya yi digiri na biyu a Electrical and Computer Engineering Universidade Nova de Lisboa, Portugal a shekara ta 2011.[1]

Sana'a gyara sashe

Borges ya shiga aikin farar hula ne a shekarar 1991 a matsayin injiniyan injiniya mai horarwa, a ENE/North Regional Directorate har zuwa shekara ta 1992 lokacin da aka naɗa shi farfesa a fannin Injiniya a Jami’ar Agostinho Neto kuma ya yi aiki tare a wasu muƙamai har zuwa shekara ta 2008 lokacin da ya zama Mataimakin Ministan Makamashi. Daga shekarun 2010 zuwa 2011, ya rike muƙamin sakataren ma'aikatar makamashi, daga shekarar 2012 zuwa yau, ya rike mukamin ministan makamashi da ruwa. [3]

Manazarta gyara sashe

  1. 1.0 1.1 Pereira, João Baptista Borges; Torres, Lilian de Lucca (2014-07-25). "Entrevista com João Baptista Borges Pereira". Ponto Urbe (14). doi:10.4000/pontourbe.1430. ISSN 1981-3341.
  2. "Portal Oficial do Governo da República de Angola - Ministro João Baptista Borges (MINEA)". SEPE - Serviços Públicos Electrónicos do Governo de Angola (in Harshen Potugis). Retrieved 2022-06-18.
  3. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-11-28. Retrieved 2023-12-06.