Jesesi Mungoshi
Jesesi Mungoshi ko kuma Jesese Mungoshi, yar'wasan kwaikwayo ce ta ƙasar Zimbabwe. Ta fara fitowa a karon farko a shekarar alif na1989, a fim mai taken, African Journey.
Jesesi Mungoshi | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Zimbabwe, |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi |
IMDb | nm0612822 |
Ayyuka
gyara sasheA farkon bayyanarta, an gabatar da Mungoshi a cikin sigar ta 1989 da kuma wacce ta biyo bayan 1990 kashi biyu na fim ɗin gidan telebijin na George Bloomfield, African Journey, wanda kuma ya haska : Jason Blicker, Katja Blomquist, Allan Jordan, Ulla Mahaka da sauransu.
A shekarar 1991, an saka ta a fim din Godwin Mawuru mai suna, Neria, inda ta fito a matsayin "Neria". Sauran 'yan wasan sune Dominic Kanaveli da Violet Ndlovu da sauransu.
Hakanan, an saka ta a cikin gajeren fim na 1993 da Farai Sevenzo mai taken, Rwendo, wanda ta fito tare da Yemi Goodman Ajibade, Ben Daniels, Eldinah Tshatedi da Frank Windsor .
A shekarar 2017, ta fito a fim din barkwanci-soyayya, Cook Off, wanda Tomas Brickhill ya bayar da umarnin, inda ta taka rawar gani a matsayin "Gogo".[1][2][3][4] Fim ɗin, kasancewar shi ne na farko da aka samar a Zimbabwe bayan dogon mulkin Robert Mugabe, an fara shi ne a Burtaniya a ranar 27 ga Yulin, 2019.[5]
Dangane da irin gudummawar da ta bayar ga masana'antar fina-finai ta Zimbabwe, an karrama ta da lambar yabo ta Rayuwa ta Babbar Jami'ar Zimbabwe a watan Mayun 2017 a Masvingo .
Fim din 2020, Shaina, wanda ta kasance tare da sauran 'yan Zimbabwe kamar: Marian Kunonga, Charmaine Mujeri da sauransu, an samu yabo sosai a kasashen waje.[6][7][8][9]
Fina-finai
gyara sasheShekara | Fim | Matsayi | Bayanan kula | Ref. |
---|---|---|---|---|
2020 | Shaina | Jaruma | [6] | |
2019 | Familiar | Jaruma | Play | [10] |
2017 | Cook Off | Actress (Gogo) | Comedy, Romance | [1] |
1993 | Rwendo | Actress | Short film, Drama | [11] |
1991 | Neria | Actress (Neria) | Drama | [12] |
1989 and 1990 | African Journey | Actress (Themba) | TV movie, Family | [13][14] |
Amincewa
gyara sasheShekara | Taron / Mai Kaya | Kyauta | Mai karɓa | Sakamakon |
---|---|---|---|---|
2017 | GZU | Kyautar Gwanin Rayuwa | style="background: #99FF99; color: black; vertical-align: middle; text-align: center; " class="yes table-yes2"|Lashewa |
Rayuwarta
gyara sasheTa auri marubuci, ɗan wasan kwaikwayo kuma mawaƙi ɗan ƙasar Zimbabwe, Charles Mungoshi, wanda, a cewar The Zimbabwe Mail da This is Africa reporters, ya mutu a ranar 16 ga Fabrairu, 2019 a Harare, Zimbabwe bayan rashin lafiya na shekaru 10 tana da shekaru 71. An albarkaci auren tare da yara biyar: Farai, Graham, Nyasha, Charles, da Tsitsi, kuma a lokacin mutuwarsa suna da jikoki bakwai.[15][16] Ma'auratan tare da ɗansu, Farai duk sun shiga harkar fim.[17]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 "Cook Off (2017)". IMDb. Retrieved November 18, 2020.
- ↑ Dray, Kayleigh. "Netflix's Cook Off: everything you need to know about this record-breaking film". Stylist. Retrieved November 19, 2020.
- ↑ "Film Review | Cook Off". New Frame. Archived from the original on January 25, 2021. Retrieved November 19, 2020.
- ↑ "DURBAN: Rising star Tendai Chitima and veteran Jesesi Mungoshi in Zim's first post-Mugabe film". New Zimbabwe. Africa News Agency. July 22, 2018. Retrieved November 19, 2020.
- ↑ "Zimbabwe's first post-Mugabe feature film - to premiere in the UK". Bulawayo24. July 25, 2019. Archived from the original on March 2, 2021. Retrieved November 19, 2020.
- ↑ 6.0 6.1 Makuwe, Munashe (August 22, 2020). "US embassy praises Zimbabwe film production, Shaina". London: New Zimbabwe. Retrieved November 19, 2020.
- ↑ "NEW MOVIE "SHAINA" DELIVERS POWERFUL HEALTH MESSAGES THROUGH A COMPELLING STORY ABOUT YOUNG ZIMBABWEANS". USAID. August 21, 2020. Archived from the original on May 23, 2021. Retrieved November 19, 2020.
- ↑ Darmalingum, Yuveshen (August 20, 2020). "ZTV TO AIR NEW MOVIE 'SHAINA' IN ZIMBABWE". NextTV Africa. Archived from the original on November 27, 2020. Retrieved November 19, 2020.
- ↑ Zimoyo, Tafadzwa (August 21, 2020). "Zimbabwe: Shaina Premières On ZBCTV Today". All Africa. Harare: The Herald. Retrieved November 19, 2020.
- ↑ "Danai Gurira play comes to Harare". The Zimbabwe Mail. September 18, 2019. Retrieved November 19, 2020.
- ↑ "Rwendo (1993)". IMDb. Retrieved November 18, 2020.
- ↑ Cite error: Invalid
<ref>
tag; no text was provided for refs namedNer
- ↑ "African Journey (1989)". IMDb. Retrieved November 19, 2020.
- ↑ "African Journey (1990)". IMDb. Retrieved November 18, 2020.
- ↑ "Author and actor Charles Mungoshi dead at 71, family announces". The Zimbabwe Mail. February 16, 2019. Retrieved November 19, 2020.
- ↑ Chatora, Andrew (February 18, 2019). "Zimbabwe: Charles Lovemore Mungoshi - Eulogy to Greatness". All Africa. Hilversum: This is Africa. Retrieved November 19, 2020.
- ↑ Moyo, Andrew (October 12, 2015). "Charles Mungoshi does the big screen". Mahanda Radio. Retrieved November 19, 2020.
Haɗin waje
gyara sashe- Jesese Mungoshi akan IMDb
- Jesese Mungoshi akan Flixable