Jeanne-Marie Ruth-Rolland
Jeanne-Marie Ruth-Rolland [1] (17 Yuni 1937 - 4 Yuni 1995) 'yar siyasar Afirka ta Tsakiya ce, ma'aikaciyar zamantakewa kuma malama. Ana daukar ta a matsayin mace ta farko da ta yi takarar shugabancin Afirka.[2]
Jeanne-Marie Ruth-Rolland | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Bangassou (en) , 17 ga Yuni, 1937 |
ƙasa | Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya |
Mutuwa | 12th arrondissement of Paris (en) , 4 ga Yuni, 1995 |
Karatu | |
Harsuna |
Faransanci Harshen Sango |
Sana'a | |
Sana'a | social worker (en) , ɗan siyasa da Malami |
Aikin Siyasa
gyara sasheRuth-Rolland ta fara aiki a matsayin mai kula da tsarin ilimi na yankin Ubangi-Shari na Faransa a 1956 da kuma mai kula da tsarin ilimin kasa na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya bayan samun 'yancin kai daga Faransa a 1960, ta ci gaba da koyarwa har zuwa 1964. Bayan haka ta kasance tayi aiki a matsayin ma'aikaciyar zamantakewa, tana taimaka wa yara kanana, kuma a matsayin shugabar sabis na zamantakewa na soja a cikin sojojin Afirka ta Tsakiya, ta bar sojojin da matsayi na shugabar bataliya.[3]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Fandos-Rius, Juan. "Parliament of the Central African Republic". Archived from the original on 18 July 2012. Retrieved 13 October 2013.
- ↑ Sheldon, Kathleen (2005). Historical Dictionary Of Women In Sub-Saharan Africa. Lanham, Maryland: Scarecrow Press. p. 217. ISBN 9780810853317.
- ↑ Kalck, Pierre (2005). Historical Dictionary of the Central African Republic (Third ed.). Lanham, Maryland: Scarecrow Press. p. 168. ISBN 0810849135.