Jean de Dieu Nkundabera ɗan wasa ne dan kasar Rwanda wanda ya fafata a wasannin motsa jiki na nakasassu. [1]

Jean de Dieu Nkundabera
Rayuwa
ƙasa Ruwanda
Sana'a
Sana'a Dan wasan tsalle-tsalle

Nkundabera ya wakilci Rwanda a gasar wasannin nakasassu ta bazara a shekarar 2004 a Athens, kuma ya lashe lambar yabo ta farko a gasar nakasassu ko na Olympics a kowane wasa, ta hanyar samun tagulla a tseren mita 800 na maza na T46, da lokacin 1:58.95. [2] Ya sake wakilci kasar Rwanda a gasar wasannin nakasassu ta lokacin zafi na shekarar 2008 a birnin Beijing. [3] [4]

Ya zuwa shekarar 2016, Nkundabera ya kasance ta daya tilo da ya lashe lambar yabo ta Olympic ko na nakasassu ta kowace iri, duk da cewa kasar Rwanda tana da yawan mutane sama da 300,000 da ke da wata nakasa. [5]

Manazarta

gyara sashe