Jean-Paul Yaovi Dosseh Abalo (an haife shi a ranar 26 ga watan Yunin shekarar 1975 a Lomé, Togo) tsohon mai tsaron ragar ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Togo kuma mai horar da 'yan wasan ƙwallon ƙafa ta ƙasar Togo a halin yanzu.

Jean-Paul Abalo
Rayuwa
Cikakken suna Yaovi Abalo
Haihuwa Lomé, 26 ga Yuni, 1975 (49 shekaru)
ƙasa Togo
Faransa
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Togo1992-2006671
OC Agaza (en) Fassara1992-1993
LB Châteauroux (en) Fassara1993-1995291
Amiens SC (en) Fassara1995-20052737
USL Dunkerque (en) Fassara2005-200540
  APOEL F.C. (en) Fassara2006-200630
Ethnikos Piraeus F.C. (en) Fassara2006-200690
Al-Merrikh SC2007-200890
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga baya
Tsayi 177 cm
Jean-Paul Abalo a cikin yan wasa

Aikin kulob

gyara sashe

Abalo ya buga wasanni shida a gasar Ligue 2 ta Faransa tare da kulob ɗin Amiens SC. [1] A cikin shekarar 2006, ya koma APOEL a Cyprus, inda ya lashe Kofin Cyprus na shekarar 2005–06. Yayin da yake a Amiens, Abalo ya taka leda a 2001 Coupe de France Final. Rashin cin bugun fenariti ne ya yanke hukunci yayin da Amiens ta sha kashi a hannun Strasbourg. [2]

Ayyukan kasa da kasa

gyara sashe

Ya kasance kyaftin na tawagar kwallon kafa ta Togo, an kira shi zuwa gasar cin kofin duniya ta shekarar 2006, kuma ya wakilci kasarsa a gasar cin kofin Afrika hudu. [3] Gudunmawar da ya bayar a gasar cin kofin duniya ta tawagar 'yan wasan ya rufe ta sakamakon jan kati da ya samu a wasan farko da Koriya ta Kudu, yayin da kungiyarsa ta sha kashi da ci 1-2.[4]

Aikin koyarwa

gyara sashe

A cikin watan Janairu 2018, an sanar da Abalo a matsayin mai horar da 'yan wasan kwallon kafa na kasa-da-20 na Togo a gasar 2018 Toulon.[5]

Girmamawa

gyara sashe

APOEL

  • Kofin Cyprus: 2005–06[6]

Manazarta

gyara sashe
  1. Samfuri:LFP
  2. Jean-Paul Abalo – French league stats at LFP – also available in FrenchEmpty citation (help)
  3. Jean-Paul AbaloFIFA competition record
  4. "Strasbourg claim Cup" . BBC. 27 May 2001. Retrieved 28 July 2016.
  5. "South Korea 2-1 Togo" . BBC . 13 June 2006. Retrieved 12 October 2021.
  6. "OFFICIEL : le Togo participera au Festival International Espoirs 2018" . Retrieved 23 January