Jayant Salgaonkar a ranar(1 ga watan Fabrairu shekara ta alif 1929 -ya mutu a ranar 20 ga watan Agusta 2013) ɗan taurari ɗan Indiya ne, ɗan kasuwa, ɗan tarihi, mawallafi kuma marubuci. An san shi da kafa Kalnirnay, kalanda da aka buga a Indiya. Kalnirnay ita ce buga mafi girma na siyarwa a duniya (almanac).[1]

Jayant Salgaonkar
Rayuwa
Haihuwa Malvan (en) Fassara, 1 ga Faburairu, 1929
ƙasa Indiya
British Raj (en) Fassara
Dominion of India (en) Fassara
Mazauni Mumbai
Mutuwa 20 ga Augusta, 2013
Sana'a
Sana'a marubuci
Jayant Salgaonkar

Ilimi da aiki

gyara sashe

An haife shi a shekara ta alif dari tara da ashirin da tara 1929 a Malvan a gundumar Sindhudurga ta Maharashtra. Salgaonkar ya yi karatunsa har zuwa aji 10. Ya kasance yana sha'awar ilimin taurari tun yana yaro. A cikin shekara ta alif dari tara da Saba'in da uku 1973, ya kafa Kalnirnay, almanac na shekara-shekara na dukan addinai yana ba da sauƙaƙan bayanai dangane da Panchang, ranaku masu kyau, bukukuwa, hutu, fitowar rana da faɗuwar rana. Ya sayar da kwafi sama da miliyan 10 a cikin harsuna tara.Shi ne majagaba na horoscope na yau da kullun da kuma kalmomin yau da kullun a cikin jaridar Marathi.[2]

Littattafai da aka buga

gyara sashe
  • Sundarmath
  • Deva Tuchi Ganeshu
  • Dharma-Shatriy Nirnay
  • Kalnirnay
  • Panchang
  • Devachiye Dwari
  • Rastyarache Dive

Kyaututtuka da karramawa

gyara sashe

Sakeshwar Vidhyapeeth da Mumbai Jyotirvidyalay sun ba shi Jyotirbhasakr. Ya rike D.Lt. daga Maharashtra Jyotish Vidyapeeth. Konkan Marathi Sahitya Parishad ya ba shi lambar yabo ta Nasarar Rayuwa. A cikin watan Mayu 2013, Saraswat Prakashan ya ba shi Saraswat Chaitanya Gaurav Purashkar.

Ya rasu ne a ranar ashirin 20 ga watan Agustan shekara ta dubu buyu da sha uku 2013 a asibitin Hinduja da ke Mahim, Mumbai bayan gajeruwar rashin lafiya. An kona shi a dakin ajiye gawa na Dadar. Bikinsa na karshe ya samu halartar shugabannin siyasa kamar Ajit Pawar, Narayan Rane, Jayant Patil, Uddhav Thackeray da Raj Thackeray. Ya rasu ya bar matarsa da ‘ya’ya maza uku.

Manazarta

gyara sashe
  1. "Founder of Kaalnirnay calendar Jyotirbhaskar Jayant Salgaonkar passes away - India - DNA". Dnaindia.com. 2013-08-20. Retrieved 2013-11-07.
  2. "Loksatta on Mobile". M.loksatta.com. Retrieved 2013-11-07.