Jamila Ashley-Cooper, Dowager Countess of Shaftesbury (née M'Barek), ita ce gwauruwar kasar Tunisiya da aka haifa a Faransa kuma mai kisan kai na 10th Earl of Shaftesburg, Yar kasar Birtaniya, kuma an ɗaure ta saboda ta biya ɗan'uwanta don kashe mijinta.

Jamila M'Barek
Rayuwa
Haihuwa Lens (en) Fassara, 1961 (63/64 shekaru)
ƙasa Faransa
Mazauni Nabeul (en) Fassara
Saint-Tropez (en) Fassara
Ƴan uwa
Abokiyar zama Anthony Ashley-Cooper, 10th Earl of Shaftesbury (en) Fassara  (5 Nuwamba, 2002 -  5 Nuwamba, 2004)
Karatu
Harsuna Faransanci
Turanci
Sana'a
Sana'a call girl (en) Fassara da aristocrat (en) Fassara
Sunan mahaifi Sarah

An haife ta a shekara ta 1961, tana ɗaya daga cikin yara bakwai da aka haifa a Lens, Pas-de-Calais,a kasar Faransa, ga iyayen baƙi, mahaifiyar kasar Tunisiya da mahaifin dake kasar Maroko. Mahaifin su mai cin zarafin ne da mugunta kuma ya Kasance Masha yin barasa wanda ke aiki a matsayin mai hakar ma'adinai.

Lokacin da Jamila M'Barek ke da shekaru shida a rayuwar ta mahaifiyarta ta gudu tare da ita da 'yan uwanta shida zuwa Nabeul, Tunisiya, don tserewa daga mahaifinsu mai cin zarafi. M'Barek ta shafe mafi yawan yarinta a can. M'Barek ta koma kasar Switzerland a farkon shekarunta na ashirin sannan ta koma kasar zuwa Paris, inda ta yi iƙirarin cewa ta yi karatun wasan kwaikwayo.

A lokacin da take da shekaru 17, M'Barek ta koma Saint-Tropez inda ta auri mijinta na farko, [1]babban dan kasuwa na Holland Raf Schouten, wanda ta haifi 'ya’ya biyu daga baya mijin ta ya sake a shekara ta 2000s. [2][3]

  1. "L'affaire de Jamila M'Barek ce soir sur France 2". babnet.net. 2010-04-17. Archived from the original on 6 June 2014. Retrieved 2010-08-14.
  2. "Lord Shaftesbury's obituary". The Daily Telegraph. 2005-04-21. Retrieved 2010-08-14.
  3. Rucker, Sam; Guyoncourt, Sally (April 24, 2024). "Jamila M'Barek now: What happened to Anthony Ashley-Cooper's wife turned killer". inews.co.uk (in Turanci).