Jamila Hammami ita ce shugabar mishan a Oman don Kungiyar Red Cross ta Duniya (ICRC). [1]

Jamila Hammami
Rayuwa
Sana'a

Jamila Hammami tayi karatu a Jami’ar Aix-Marseille . Ta fara aiki da ICRC a shekara ta 2002. A shekara ta 2008 ta yi kira kuma ga hukumomin Iraki da su nemo iyalan sojojin Iraki guda 62 wadanda aka dawo da kuma gawarwakinsu daga Saudiyya . [2] Daga baya kuma a waccan shekarar ta taimaka ta tsara musayar ragowar sojoji kusan 250 da aka kashe a yakin Iran-Iraq . [3] A cikin shekara ta 2010 da shekara ta 2011 tana aiki a Kathmandu, tana ba da taimako kuma na wucin gadi ga waɗanda suka tsira daga Yaƙin basasar Nepalese . [4] [5] A cikin shekara ta 2014-5 ta shugabanci ƙungiyar ICRC a Tripoli, Lebanon, tare da yin aiki tare da al'ummomin da rikice-rikicen makamai suka shafa daga yaƙin Siriya . [6]

Manazarta

gyara sashe
  1. Sebastian Castelier, Oman’s humanitarian aid to Yemen also pragmatic, Al-Monitor, January 9, 2020. Accessed March 14, 2020.
  2. Saudi returns bodies of Iraqis killed in Gulf War[permanent dead link], Reuters, April 3, 2008. Accessed March 14, 2020.
  3. Red Cross brokers swap of Iranian and Iraqi war dead Archived 2021-06-04 at the Wayback Machine, The Daily Star, December 1, 2008. Accessed March 14, 2020.
  4. Relatives of the missing struggle with legal void, social taboo, The New Humanitarian, December 29, 2010. Accessed March 14, 2020.
  5. Brendan Brady, The Ghosts of Nepal’s ‘Disappeared’, The Diplomat, March 26, 2011. Accessed March 14, 2020.
  6. Lebanon: Strengthening the resilience of communities affected by violence, ICRC, February 11, 2015. Accessed March 14, 2020.