Idakwo Ameh Oboni II
Idakwo Michael Ameh Oboni II (1948 - Agusta 27, 2020)[1] ya kasance Sarki na 27, Àtá Ígálá (masarauta mafi girma) na Masarautar Igala da ke a Tsakiyar Najeriya.[2][3]
Idakwo Ameh Oboni II | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 1948 |
Mutuwa | 27 ga Augusta, 2020 |
Sana'a |
Rayuwa da ilimi
gyara sasheAn haifi Oboni II a shekarar 1948. A 1960, ya kammala karatunsa na firamare a Saint Boniface da ke Idah. Daga nan ya ci gaba zuwa Kwalejin Saint Augustine, Kabba, inda ya kammala a 1967.[4] Daga nan ya wuce Kaduna Polytechnic har wayau ya kammala karatunsa da satifiket na shedar Estate Management a shekarar 1980.[4]
Aiki
gyara sasheDaga nan ya shiga aikin sojan saman Najeriya a shekarar 1968 ya bar aikin a radin kansa a shekarar 1974. Bayan nan ya yi aiki a matsayin jami’in duba filaye a ma’aikatar filaye a tsohuwar jihar Kwara sannan ya bar aiki a shekarar 1975 don neman ilimi. A shekarar 1981, ya fara Aiki a hukumar raya babban birnin tarayya (FCDA) kuma a tsawon shekaru, ya kai matsayin mataimakin darakta, inda ya yi ritaya a shekarar 2006.[4]
Mulki
gyara sasheBayan mutuwar 26th Àtá Igala Àtá Àlíì Ọ̀chẹ́ja Òtúlúkpé Ọ̀bàje a shekara ta 2012,[5] An zaɓi Àám̀ gaba ɗaya daga cikin gidaje huɗu masu mulki a Anɛ Igálá a matsayin magajin sarauta. An miƙa naɗin nasa ga Sarakunan Igalamela tara (9) a matsayin wani ɓangare na tsarin gargajiya al'adar masarautar. Masu sarauta sun amince da naɗin nasa don aikawa zuwa ga Achadu oko-Ata (Firayim Minista Igala).[6] An miƙa amincewar sa da firaministan Igala ya yi ga majalisar gargajiya ta jihar Kogi daga karshe gwamnan jihar kogi Capt Idris Ichala Wada ya amince da shi.[7] Ya furta cewa shi ne Ata na farko da ya auri mace ɗaya a tarihin ƙasar Igala.[4]
Da zuwan gwamnatin Buhari a Najeriya, HRM Ameh Oboni II a shekarar 2016 a garin Idah, yayin bikin cikar sa karo na uku kan ƙaragar mulki, ya ɗora wa shugaban kasa "ya fara canza sheka a jihar Kogi".[8]
Bayan zaɓen 2019 da tashe-tashen hankula suka biyo bayan zaɓen 2019, ƙungiyar Àtá Igálá ta la'anci waɗanda suka aikata ta'addancin zaɓe a jihar.[9]
Dabi'u
gyara sasheAn bayyana shi a matsayin mutum mai son zaman lafiya kuma mai ba da shawarwari masu kyau da kuma sanannen gaskiya. Dansa, Prince Ocholi Idakwo ya bayyana shi a matsayin "mutum mai aiki kuma mai kishin raya al'adun Igala".[10]
Mutuwa
gyara sasheRahotanni sun ce ya rasu ne a safiyar ranar Alhamis 27 ga watan Agustan 2020 bayan ɗan gajeran mulki na kimanin shekaru takwas, wanda ya fara bayan rasuwar magabacinsa wanda ya yi mulki na tsawon shekaru 52.[11] Oboni II ya rasu ne a wani asibitin Abuja bayan da aka yi masa tiyatar da ba'a yi nasara ba.[4]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Attah of Igala,Dr.Aliyu Obaje is dead". Newsdiaryonline. July 16, 2012. Retrieved 11 October 2013.
- ↑ "Buhari mourns Attah Igala, Michael Oboni II". Premium Times Nigeria. August 30, 2020. Retrieved September 25, 2020.
- ↑ Moribirin, Rosemary (August 27, 2020). "Breaking: In Kogi, Attah of Igala is dead". Blueprint. Retrieved September 25, 2020.
- ↑ 4.0 4.1 4.2 4.3 4.4 "Ameh, Attah Igala, dies during operation in Abuja". The Cable. August 27, 2020. Retrieved September 25, 2020.
- ↑ "Attah Igala, Aliyu Obaje dies at 102 | Premium Times Nigeria" (in Turanci). 2012-07-17. Retrieved 2022-03-03.
- ↑ "Intrigues as race for Attah Igala stool heats up". Daily Trust (in Turanci). 2020-11-15. Retrieved 2022-09-18.
- ↑ Ottah, Gabriel Alhassan (2015-10-27). "African Culture and Communication Systems in the Coronation of Ata Igala, North- Central Nigeria". AFRREV IJAH: An International Journal of Arts and Humanities (in Turanci). 4 (3): 208–228. doi:10.4314/ijah.v4i3.18. ISSN 2227-5452.
- ↑ Sule, Itodo Daniel (March 30, 2016). "Nigeria: Attah Igala Tasks Buhari On Change Mantra". All Africa. Daily Trust (Abuja). Retrieved September 25, 2020.
- ↑ "Dr Michael Idakwo Ameh Oboni 11 Attah Igala places ancestral curse on perpetrators of electoral violence". The Guardian. March 3, 2019. Retrieved September 25, 2020.
- ↑ Olaniyi, Muideen (August 29, 2020). "Buhari: Late Attah Igala, Ameh Oboni II, Was A Man Of Peace". Daily Trust. Retrieved September 25, 2020.
- ↑ "Attah of Igala, Idakwo Ameh Oboni II, passes away". KAFTANPost. August 27, 2020. Retrieved September 25, 2020.