Ibife Alufohai
Ibife Eugene Alufohai (an haife ta ranar 29 ga watan Agustan shekarar 1986) 'yar Nijeriya ce, 'yar kwalliya, mai aikin bada agaji, mai kuma riƙe da kambun sarauniyar kyau ta Miss Valentine International 2010. Ita ce ta kirkiro Miss Polo International.
Ibife Alufohai | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Calabar, 29 ga Augusta, 1986 (38 shekaru) |
Sana'a |
Tarihin Rayuwa
gyara sasheAlufohai ta fito ne daga garin Abonnema na, jihar Ribas. Sai dai an haife ta ne a Calabar, Jihar Kuros Riba kuma ita ce ta ƙarshe cikin yara bakwai na iyayenta. Iyalinta sun yi kaurace-kaurace sosai saboda yanayin aikin mahaifinta a matsayin jami'in soja, wanda aka yi ta yiwa sauyin wajen aikin daga jihar Kaduna suka koma Fatakwal, zuwa Jihar Ribas.
Karatu
gyara sasheDaga shekarar 1993 zuwa 1997 ta yi karatunta na firamare, ta kuma fara na sakandare duk a makarantar Tantua International Group of Schools inda ta kammala a shekarar 2003. A kuma shekarar 2003 din ta tafi Jami'ar Madonna, Okija don karatun jami'a sannan ta wuce Jami'ar Fatakwal, Jihar Ribas a shekarar 2008, inda ta kammala a shekarar 2012 tare da digiri a fannin Clinical psychology . Bayan karatun ta na jami'a, ta yi bautar kasa a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Yenagoa, Jihar Bayelsa, inda ta yi aiki a matsayin masaniyar halayyar dan Adam da kuma aiki a ECG daga shekarun 2013 zuwa 2014.
Iyali
gyara sasheAlufohai ta yi aure har da diyar ta. A zaman wani bangare na ayyukan taimakon al'umma da take, ta kafa gidauniya mai suna Polo International Relief Foundation.
Manazarta
gyara sashe