Hukumar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta Najeriya

Babbar Kungiyar motsa jiki ce a Najeriya

Hukumar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta Najeriya hukuma ce da ke kula da harkokin wasannin motsa jiki a Najeriya. Memba ce ta kungiyar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta Afirka da kuma kungiyar 'yan wasa ta kasa da kasa.

Hukumar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta Najeriya
Bayanai
Iri sports governing body (en) Fassara
Ƙasa Najeriya
Mulki
Hedkwata Abuja
Tarihi
Ƙirƙira 1944
athleticsnigeria.org

An kafa ta a matsayin Babban Kwamitin Ƙwararrun na Nijeriya a shekarar 1944.[1] Kungiyar ta AFN tana da hedikwata ne a babban filin wasa na Najeriya dake Garki, Abuja.[2]

Shirye-shirye

gyara sashe

Tana shirya gasar AFN Golden League na shekara-shekara wanda gasar cikin gida ce mai kama da tsarin IAAF Golden League na yanzu.

Shugabanta shine Ibrahim Shehu Gusau ne tun a shekarar 2017 har zuwa yau.[1]

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 "About AFN | The Athletics Federation of Nigeria|AFN". Athleticsnigeria.org. Archived from the original on 2012-08-01. Retrieved 2012-05-27.
  2. "The Athletics Federation of Nigeria|AFN|Welcome to the official home of Athletics in Nigeria". Athleticsnigeria.org. Archived from the original on 2011-06-24. Retrieved 2012-05-27.

Hanyoyin haɗi na waje

gyara sashe