Yusuf Abdullahi Falgore
Yusuf Abdullahi Falgore (An haifeshi a shekarar 1953) a garin Falgore dake karamar hukumar Rogo ta jihar Kano.
Farkon rayuwa da Karatu
gyara sasheAn haifesh a garin Falgore, na karamar hukumar Rogo, Jihar Kano a Najeriya.
Yayi makarantar Falgore Central primary a shekarar 1963 – 1969 sannan ya halarci Gwarzo Senior Primary School. Daga nan ya wuce Kwalejin Malamai ta Bichi a shekarar 1970 kuma ya kammala a shekarar 1974. [1]
Daga shekarar 1975 – 1978 ya halarci Makarantar Advance Teachers College, Zariya, ya kuma fito da takardar shaidar karatu ta ƙasa (NCE). Daga nan ya wuce Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarar (1981 – 1983) don yin digiri a fannin Ilimi.
Aiki
gyara sasheKafin ya shiga siyasa Yusuf Falgore ma’aikaci ne a ma’aikatar ilimi ta jihar Kano. [2]
Falgore shine tsohon kakakin majalisar Jihar kano kuma shi ne Shugaban Kwamitin Gudanarwa da Nasiha tsakanin shekarar 2011-2015 ya jagoranci Kwamitin Majalisar kan Ilimin Sakandare.
Siyasa
gyara sasheAn zaɓi Falgore a matsayin Shugaban Ƙaramar Hukuma batare da Jam’iyya ba, sannan ya zama Shugaban riko (Sau biyu) A shekarar 1991 – 1993, da kuma shekarar 2002 – 2003 bi da bi. [3] An zaɓe shi a matsayin ɗan Majalisar Dokoki ta Jihar kano sau biyu, 2011 – 2015 sai 2015 – 2019 bi da bi, kuma ya rike kakakin majalisar jahar kano na yan watanni kafin a tsigeshi a maye gurbinsa da Gambo Sallau a shekarar 2011.