Hayin na'iya
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
. |
Hayin na'iya unguwace sabuwa wacce aka ƙirƙireta shekaru kaɗan dasuka gabata, tana cikin Kaduna ne karkashin karamar hukumar Igabi. wanda take raɓe/haɗe da Rafin guza kuma tana kewaye da unguwanni kamar haka, daga gabas akwai malalin gabas da kukumake, akwai NDC daga yamma College of petroleum, sai mangwaron agwai haka kuma tana da manyan layika kamar su layin zaurawa, layin jarƙasa, faskari road, dadai sauran su. Unguwan na da makaranta L.E.A firamare, ana kiranta L.E.A hayin na'iya, inda yaran gari ke gudanar da karatunsu na zamani a gomnatance haka tanada makarantar koyar da ilimin addini masu tarin yawa. Haka tana da ido sosai a ɓangaren kasuwanci inda kullum ake ɓuɗe sabbin shaguna domin gudanar da kasuwanci. Hayin na'iya nada dogon titi wanda ya ratsa ta cikinta daga Rafin guza zuwa malalin gabas.