Hauwa Ayawa jaruma ce a masana'antar fim ta Hausa wato masana'antar Kannywood, tayi fina finai da dama a masana'antar fim, ta fito a fim ɗin tashar arewa 24 Mai suna GIDAN BADAMASI, inda ta fito a yar Autar alhaji badamasi Mai suna azima.[1]

Hauwa Abubakar Ayawa haifaffiyar Jihar Kaduna ce an haifeta a shekaran 1994.[2] ta girma a jihar kaduna tayi karatun firamare a jihar kaduna, daga nan ta tafi jihar zamfara tayi sakandiri a makarantar gwamnatin mata Dake cikin kwatarkwashi. Bayan kammala sakandiri tayi karatun kwamfuta. Jarumar Bata da aure[3]

Hauwa tace ta fara ne sakamakon mahaifiyar ta mai shirya finafinai ce a masana'antar tana ganin jarumai a gidan su kala kala, tana da sha'awar yin fim ɗin. An fara hadata da fitaccen Mai Bada umarni muhammad alfazazi inda yasa ta a wasanin barkwanci, daga nan falalu dorayi yaga yadda take aktin ya dauke ta ya SATA a fim din sa na Gidan badamasi.wanda shine tushen daukakarta. Fim dinta na farko shine fim ɗin musaddiq Wanda mustapha m Shariff ya Bada umarni, daga Nan SE fim ɗin karar kwana.

Manazarta

gyara sashe
  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-29. Retrieved 2023-07-29.
  2. https://manuniya.com/2022/12/09/cikakken-tarihin-azeema-gidan-badamasi/
  3. https://aminiya.ng/ban-taba-tunanin-zan-yi-tashe-kamar-haka-ba-azeema/