Hari a wurin Jana'iza a Kuda
Harin yan Boko Haram a Najeriya ranar 16 ga watan Yunin 2016
A ranar 16 ga watan Yunin 2016 ne ƙungiyar Boko Haram ta kai wani hari a wani wurin jana’iza a Kuda, Najeriya.[1][2]
Hari a wurin Jana'iza a Kuda | ||||
---|---|---|---|---|
attack (en) | ||||
Bayanai | ||||
Kwanan wata | 16 ga Yuni, 2016 | |||
Perpetrator (en) | Boko Haram | |||
Wuri | ||||
|
Lamarin
gyara sasheA yammacin ranar 16 ga watan Yunin 2016 ne wasu gungun ‘yan bindiga daga ƙungiyar Boko Haram masu da’awar jihadi suka isa Kuda, wani ƙauye kusa da Madagali a arewacin jihar Adamawa da ke a arewa maso gabashin Najeriya, bisa babura.[1][2] A lokacin ana jana'izar wani shugaban yankin. [1][2] Ƴan ta’addan sun buɗe wuta kan masu jana'izar inda suka kashe aƙalla 18 daga cikinsu tare da jikkata wasu aƙalla 10.[1][2] Maharan sun kuma yi awon gaba da abinci tare da ƙona gidaje.[1][2]
A baya ƙungiyar Boko Haram sun kai hari a wannan kauyan a watan Fabrairun 2016.[2]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 "Boko Haram murder 24 at village funeral – mostly women". The Guardian. 2016-06-17. Archived from the original on 2022-12-09.
- ↑ 2.0 2.1 2.2 2.3 2.4 2.5 "Boko Haram kills 18 women at a funeral in Nigeria". Al Jazeera. Archived from the original on 2023-07-10.