Hamid Ait Bighrade
Hamid Ait Bighrade (an haife shi a ranar goma sha uku ga watan Mayu shekara ta 1976) ɗan wasan damben ƙasar Morocco ne wanda ya fafata a gasar Olympics ta bazara ta 2004 a Athens. [1]
Ait Bighade ya cancanci yin dambe a gasar Olympics ta bazara ta 2004 ta hanyar lashe lambar zinare a gasar neman cancantar shiga gasar Olympics ta Afirka ta 2 na AIBA a Gaborone, Botswana ta doke Abel Aferalign na Habasha . [2]
Ait Bighrade yayi yaƙi a matsayin bantamweight a gasar Olympics ta 2004 . Ya yi rashin nasara a zagayen farko a hukuncin da aka yanke da 25 – 17 a kan Diwakar Prasad na Indiya. [3]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Hamid Ait Bighrade Biography and Olympic Results". Sports-Reference.com. Archived from the original on 4 November 2012.
- ↑ "African Olympic Qualifications - Gaborone, Botswana - March 15–22, 2004". amateur-boxing.strefa.pl. Archived from the original on 11 August 2011.
- ↑ "Diwakar in second round, Akhil Kumar out". The Times of India. 18 August 2004. Archived from the original on 3 November 2012.