Hadizatou Mani
Hadizatou Mani (an haife ta a shekara ta 1984) ƴar fafutukar kare haƙƙin bil adama ce daga Nijar da ta yi fafutukar 'yantar da kanta daga bauta a kotunan shari'a.
Hadizatou Mani | |
---|---|
mutum | |
Bayanai | |
Jinsi | mace |
Ƙasar asali | Nijar |
Shekarun haihuwa | 1984 |
Wurin haihuwa | Yankin Tahoua |
Harsuna | Faransanci |
Sana'a | Mai kare ƴancin ɗan'adam |
Kyauta ta samu | International Women of Courage Award (en) da BBC 100 Women (en) |
Rayuwa
gyara sasheAn haifi Mani a shekara ta 1984 a Nijar. An sayar da ita a bauta/baiwa tana da shekaru goma sha biyu akan dala 500. Bauta haramun ce a Nijar, amma kuma tun daga shekara ta 2003, kuma har yanzu ana bayyana shi. An sanya ta aiki kuma ta haifi 'ya'ya uku ga maigidanta. Ya yi da'awar cewa ita matarsa ce ba kuyangarsa ba. Hakan ya sa ya zarge ta da bigamy lokacin da ta auri wani. An tura Mani gidan yari na tsawon watanni shida amma an ƙarfafa mata gwiwa ta ɗaukaka ƙara.[1]
Bayan da ta yi amfani da kotuna wajen soke hukuncin da aka yanke mata an ba ta diyyar dala 20,000 sannan aka karrama ta da lambar yabo ta mata masu ƙarfin gwiwa ta duniya a shekarar 2009.[2] Ta kasance cikin jerin mutane 100 mafi tasiri a duniya na[1] 2009 na Time Magazine kuma an karrama ta a matsayin ɗaya daga cikin Mata 100 na BBC a cikin Disamba 2022.[3]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 https://web.archive.org/web/20090503145032/http://www.time.com/time/specials/packages/article/0,28804,1894410_1894289_1894358,00.html
- ↑ https://web.archive.org/web/20090502195543/http://blogs.state.gov/index.php/entries/hadizatou_mani/
- ↑ https://www.bbc.co.uk/news/resources/idt-75af095e-21f7-41b0-9c5f-a96a5e0615c1