Dr. Habibu Sani Ɓaɓura (An haifeshi ranar [yaushe?] ga watan Janairun shekarar 1952) a garin Babura Dake Jihar Jigawa.[1]

Dr Habibu Ya Zana Jarabawar "WAEC" A Shekarar 1972 Inda Ya Tafi Jami'ar Amadu Bello Zaria Yayi Karatun Share Fagen Shiga Jami'a Na Watanni 18, Kana Daga Bisani Ya Fara Karatun Digiri A bangaren Hausa Kuma Ya Kammala A shekarar 1977, Dr Habibu Sani Yana Daya Daga Cikin Rukunin Dalibai Na 4 Da Suka Fara Karantar Harshen Hausa A Duk Fadin Najeriya, Bayan Da Dr Habibu Sani Ya Kammala Karatun Digiri A ABU Zaria,Ya Tafi Bautar Kasa (NYSC) A Jihar Borno A Shekarar (1977-1978).

Dr Habibu Sani Ya Samun Aikin Koyarwa A Jami'ar Bayero Dake Kano Inda Ya Shafe Shekaru 38 Yana Koyarwa A Jami'ar BUK Kano.

Bayan Fage

gyara sashe

Hatsarin mota

gyara sashe

Dr Habibu Ya Gamu Da Hatsarin Mota A Shekarar 1982 A Titin Kabuga, Akan Hanyarshi Ta Zuwa Wurin Aikinsa A jami'ar Bayero University Kano, Inda Hakan yayi sanadiyar Mutuwar Shenyewar Jiki, Wanda Hakan Tasa Dole Sai Dai Ana Turashi A Kujerar Guragu (Wheelchair). [2] Taimakonsa Ga Al'umma.

Dr Habibu ya taka rawa gani wajen ɗaukar nauyin karatun yara daga jahar Jigawa Musamman "Yan Asalin Garinsu Na Babura Inda Gidanshi Ya Koma Gidan Dalibai, Ma'ana duk wasu Dalibai da sukazo daga Babura Kuma Suka rasa wurin kwana a Jami'ar Bayero Kano, Tu Sai Su Koma Gidan Dr Habibu da Zama.

Babban abun mamaki ga rayuwar Dr Habibu Sani Babura, Shine Lalurar Da Ta Sameshi Da Mutuwar Jiki,Amma Hakan bai hanashi aikinsa da bayar da gudunmawa ga Al'umma ba.[3]

Dr Habibu Sani Babura ya rasu Rasu Ranar 4/09/2018.

Manazarta

gyara sashe