Guilherme Afonso
Guilherme Afonso (an haife shi a ranar goma sha biyar 15 ga watan Nuwamba, shekarar dubu ɗaya da ɗari tara da tamanin da biyar 1985) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan gaba ga kungiyar kwallon kafa ta Mendrisio-Stabio. Yana da shaidar ɗan ƙasa biyu na Angolan-Swiss.[1][2]
Guilherme Afonso | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Luanda, 15 Nuwamba, 1985 (39 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa |
Angola Switzerland | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harsuna | Portuguese language | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Mahalarcin
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Ataka | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Lamban wasa | 23 | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Nauyi | 77 kg | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 188 cm |
Aikin kulob
gyara sasheAfonso ya buga wasan ƙwallon ƙafa a Switzerland a kulob ɗin Étoile Carouge, Sion, Grasshopper, Lugano da FC Vaduz; a Faransa kulob ɗin Valence; kuma a cikin Netherlands a ƙungiyoyin FC Twente da BV Veendam. [3] [4] [5] A cikin shekarar dubu biyu da tara 2009 ya zira kwallon da ya ci nasara yayin da Sion ta doke BSC Young Boys da ci ukku da biyu 3-2 a gasar cin kofin Swiss. [6]
A lokacin rani shekarar dubu biyu da goma sha biyu 2012 ya sanya hannu kan kwangilar shekaru biyu tare da kulob ɗin FC Vaduz. A lokacin rani na shekarar dubu biyu da goma sha ukku 2013 ya sanya hannu a kwangilar shekara guda da rabi tare da kulob ɗin Primeiro de Agosto. [7]
Afonso ya sanya hannu tare a kulob ɗin Mendrisio-Stabio a cikin watan Disamba, shekarar dubu biyu da goma sha takwas 2018. [8]
Ayyukan kasa da kasa
gyara sasheAfonso, wanda a baya ya taba bugawa kasar Switzerland wasa a matakin kasa da 'yan shekara 21, Angola ce ta zabi shi a gasar cin kofin kasashen Afrika na shekarar 2013.[9]
Kwallayen kasa da kasa
gyara sashe- Maki da sakamakon da Angola ta ci ta farko. [10]
A'a | Kwanan wata | Wuri | Abokin hamayya | Ci | Sakamako | Gasa |
---|---|---|---|---|---|---|
1. | 7 ga Yuni 2013 | Estádio 11 de Novembro, Luanda, Angola | </img> Senegal | 1-0 | 1-1 | 2014 cancantar shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA |
2. | 7 ga Satumba, 2013 | Estádio Nacional da Tundavala, Lubango, Angola | </img> Laberiya | 3-0 | 4–1 | 2014 cancantar shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA |
Girmamawa
gyara sasheSion
- Kofin Swiss : 2008-09
Manazarta
gyara sashe- ↑ Tope Agboola (20 June 2005). "Afonso eyes Angola switch" . BBC Sport.
- ↑ "Football without borders in the Lowlands" . FIFA. 30 June 2005. Archived from the original on 1 October 2007.
- ↑ (in Dutch) Profile at Voetbal International Archived 2016-02-27 at the Wayback Machine
- ↑ (in German) Profile at Weltfußball.de
- ↑ (in Dutch) Profile at Ronald Zwiers Archived 2016-03-03 at the Wayback Machine
- ↑ "Switzerland Cup Details" . RSSSF. Retrieved 18 August 2022.
- ↑ "Guilherme Afonso pledges commitment to new club" . ANGOP. Retrieved 1 August 2013.
- ↑ Altro colpaccio del Mendrisio, arriva la punta Guilherme Afonso!, chalcio.com, 21 December 2018
- ↑ "Angola pick Guilherme Afonso in final Nations Cup squad" . BBC Sport. 8 January 2013.
- ↑ "Guilherme Afonso". National Football Teams. Benjamin Strack-Zimmerman. Retrieved 19 April 2017.