Gong Li ( Sinanci : 巩俐; an haife ta a ranar 31 ga watan Disamba, 1965) 'yar fim ce' yar asalin ƙasar Singafo wacce aka haifa a kasar Sin, ana daukarta a matsayin daya daga cikin kyawawan mata a China a yau. Ta yi fice a cikin uku daga cikin Kyaututtuka huɗu na Finafinan duniya mafi kayatarwa da aka yi su da yaren China.

Gong Li
member of the National Committee of the Chinese People's Political Consultative Conference (en) Fassara

1998 -
Rayuwa
Haihuwa Shenyang (en) Fassara, 31 Disamba 1965 (58 shekaru)
ƙasa Sin
Singapore
Ƴan uwa
Abokiyar zama Ooi Hoe Seong (en) Fassara  (Nuwamba, 1996 -  2010)
Jean-Michel Jarre (en) Fassara  (2019 -
Ma'aurata Zhang Yimou (en) Fassara
Karatu
Makaranta Central Academy of Drama (en) Fassara
(1985 -
Harsuna Sinanci
Faransanci
Sana'a
Sana'a Jarumi da ɗan wasan kwaikwayo
Tsayi 1.6 m
Muhimman ayyuka Red Sorghum (en) Fassara
Raise the Red Lantern (en) Fassara
Memoirs of a Geisha (en) Fassara
Farewell My Concubine (en) Fassara
The Story of Qiu Ju (en) Fassara
Kyaututtuka
IMDb nm0000084

Kuruciya gyara sashe

An haifi Gong Li ne a garin Shenyang, Liaoning, China, ita ce auta a jerin yara biyar din da iyayenta suka haifa. Mahaifinta farfesa ne a fannin tattalin arziki kuma mahaifiyar ta malama ce. Ta girma ne a Jinan, babban birnin Shandong . Ta kasance mai son waƙa da rawa tun tana ƙarama, kuma tana da burin zama mawaƙiya.

Aiki gyara sashe

1987–1989: Farawar aikinta gyara sashe

A shekarar 1987, wani darakta mai suna Zhang Yimou ya fara zabar Gong don taka rawa a cikin wani shirin yakin nuna kin jinin Japan mai suna Red Sorghum, wanda a hukumance ya kaddamar da hadin kansu na tsawon shekaru 15 tare da daraktocin ƙarni na biyar na kasar Sin. Fim din ya lashe Gwarzon Zinare a bikin Fim na Kasa da Kasa karo na 38 a Berlin, ya zama fim din kasar Sin na farko da ya fara samun wannan kyauta. Hakanan ya sami lambar yabo ta Golden Rooster da Kyautar Furanni Dari a matsayin fim Mafi Kyawun Hoto a cikin 1988.

Manazarta gyara sashe