Gilbert Mapemba
Gilbert Mapemba (an haife shi a ranar 26 ga watan Yulin 1985) ɗan wasan baya ne na Zimbabwe, gabaɗaya yana wasa a gefen dama.
Gilbert Mapemba | |||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||
Haihuwa | 26 ga Yuli, 1985 (39 shekaru) | ||||||||||||||||||||||
ƙasa | Zimbabwe | ||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Mai buga baya |
Sana'a
gyara sasheMapemba ya fara aikinsa a Circle Cement FC (Zimbabwe), yana buga wasa a can daga shekarun 2003 zuwa 2004. Sannan ya buga wa Buymore FC wasa tsakanin shekarun 2005 zuwa 2007. Daga nan ya koma CAPS United FC daga shekarun 2008 zuwa 2011. Daga nan ya ci gaba da shiga kungiyar Moroka Swallows taAfirka ta Kudu, inda ya rattaba hannu kan yarjejeniyar shekaru uku. Ya kasance cikin tawagar Moroka Swallows wacce ta kare a matsayi na biyu a gasar Premier na cikin gida na kakar 2011-2012, kuma wacce ta lashe MTN8 a shekarar 2012.
Ba a sabunta kwantiragin Mapemba da Moroka Swallows ba saboda "manufofin 'yan wasan waje 5" a gasar Premier ta Afirka ta Kudu, yayin da tawagar ta so ta kara 'yan wasan kasashen waje. A halin yanzu shi wakili ne na kyauta (ɗan wasan da bashi da kulob).[1]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Soccer player database, Soccer club database - Soccer Wiki: For the fans, by the fans" .
Hanyoyin haɗi na waje
gyara sashe- Gilbert Mapemba at National-Football-Teams.com
- Gilbert Mapemba at Soccerway