Gidan Tarihi na MF Sumtsov Kharkiv

Gidan Tarihi na MF Sumtsov Kharkiv (Ukraine : Харківський історичний музей імені М. Ф. Сумцова, Kharkivskyi Istorychnyi Muzei Imeni MF Sumtsova ) gidan kayan gargajiya ne na tarihi da ke Kharkiv, Ukraine. An sadaukar da shi ga tarihi da al'adun Ukraine da kabilun da ke zaune a nan.

Gidan Tarihi na MF Sumtsov Kharkiv
Харківський історичний музей імені М. Ф. Сумцова
Харківський історичний музей
Музей Слобожанщини
Український державний історичний музей імені Г. С. Сковороди
Музей Слобідської України імені Г. С. Сковороди
Wuri
Ƴantacciyar ƙasaUkraniya
Oblast of Ukraine (en) FassaraKharkiv Oblast (en) Fassara
Raion of Ukraine (en) FassaraKharkiv Raion (en) Fassara
Centre of oblast (en) FassaraKharkiv
Coordinates 49°59′33″N 36°13′50″E / 49.9925°N 36.2306°E / 49.9925; 36.2306
Map
History and use
Opening21 ga Janairu, 1920
Shugaba Soshnikova Olha Mykolaivna (en) Fassara
Mykola Sumtsov (en) Fassara
Volodymyr Tsyhulov (en) Fassara
Suna saboda Mykola Sumtsov (en) Fassara
Hryhorii Skovoroda (en) Fassara
Heritage
Collection size 336,000
Visitors per year (en) Fassara 230,000
Contact
Address вул. Університетська, 5, м. Харків, 61003, Україна, Universytetska str. 5, Kharkiv, 61003, Ukraine da ул. Университетская, 5
Email mailto:mail@museum.kh.ua
Waya tel:+380-57-731-2094
Offical website
Gidan kayan tarihi na Kharkiv
Hoton populist V. Tikhotsky.

Mykola Sumtsov ne ya kafa gidan kayan tarihin a 1920 l a matsayin Gidan Tarihi na Sloboda Ukraine ( Музей Слобідської України ). Ya dauke da mafiya kyawun kayan tarihi daga Jami'ar Kharkiv da gidan kayan tarihi na fasaha da masana'antu na birni.

An fara tattara kayan tarihi na Jami'ar Kharkiv a shekarar 1804. An yi amfani da kayayyakin wajen koyar da ɗalibanta. Wannan tarin ya kasance ɗaya daga cikin tarin kayan tarihi na farko a Ukraine. An kafa gidan kayan gargajiya na Fasaha da Masana'antu a shekarar 1886. Kayayyakinta na gargajiya na ɗaya daga cikin mafi girma kuma mafi kyawu na daukakin gidajen tarihi na birni a cikin Daular Rasha. A cikin 1902 an gudanar da taron Archaeological Congress a Kharkiv. An gudanar da gagarumin bincike na nema kayan tarihi. An tattara adadin abubuwa masu mahimmanci na tarihi da dama, kayayyakin amfani na gida, wanda ya bayyana tarihi da al'adun mazauna yankin. Ga mahalarta taron an ƙirƙiri nune-nunen ne don nuna waɗannan abubuwa. Daga baya mafi yawan abubuwa sun zama wani ɓangare na kayan tarihin MF Sumtsov Kharkiv Tarihi Museum. Yaƙin Duniya na Biyu yayi mummunan rauni ga tarin kayan tarihin. A wannan lokacin an yi asarar wani muhimmin sashi na tarin.

A ranar 18 ga watan Yuni, 2015, an sanya ma gidan kayan tarihin suna a bayan wanda ya kafa ta kuma darekta na farko - Mykola Sumtsov . Har ila yau gidan tarihi na MF Sumtsov Kharkiv na da mahimmanci ta fuskar bincike, binciken irin na kimiyya da ilimin al'adu na yankin Kharkiv.

nune-nunen

gyara sashe
  • Archaeology na Kharkiv yankin
  • Kharkiv yankin a lokacin tsakiyar zamanai da kuma cossack zamanin
  • Al'adun kabilanci na yankin Kharkiv
  • zamanin Cossack a cikin tarihin Ukrainian
  • Kharkiv a cikin karni na 19
  • Kharkivites a gaban yakin duniya na daya (1914-1918)
  • Yankin Kharkiv a cikin juyin juya halin 1917 da lokacin interwar (1917-1940)
  • Yaƙin Duniya І
  • Kharkiv a zamanin Soviet 1943-1991
  • Ayyukan anti ta'addanci da yankin Kharkiv

Duba kuma

gyara sashe
  • Mykola Sumtsov

Hanyoyin haɗi na waje

gyara sashe