Gidan Kayan Tarihi Na Okoroji House

Gidan tarihi na Okoroji House ko Gidan Okoroji, (Igbo: Ulo Nta Okoroji, Ogbuti Okoroji), wani gida ne mai cike da tarihi da kayan tarihi dake Ujari, a ƙauyen Arochukwu, Jihar Abia, Gabashin Najeriya. [1] Hukumar kula da gidajen tarihi da tarihi ta kasa ta ayyana gidan a matsayin ababen tarihi na kasa a shekarar 1972.[2]

Kallon waje na gidan Chief Okoroji

Tarihi da tsari

gyara sashe

Maazi Okoroji Oti, wani basarake kuma ɗan kasuwan bayi ne ya gina gidan a ƙarni na 17. Gidan an yi shi da laka yayin da rufin ya kasance da aluminum zinc. Gidan yana baje kolin abubuwa masu tsarki iri-iri, kayan tarihi, sarƙoƙi na bayi, manilan tagulla, takuba da bindigogi.[3] [4]

Manazarta

gyara sashe
  1. Uguru, Okorie (27 June 2015). "Okoroji House Gateway to the past". The Nation News. Retrieved 1 September 2016.Uguru, Okorie (27 June 2015). "Okoroji House Gateway to the past" . The Nation News . Retrieved 1 September 2016.
  2. G. Ugo Nwokeji (13 September 2010). The Slave Trade and Culture in the Bight of Biafra: An African Society in the Atlantic World . Cambridge University Press. pp. 104–. ISBN 978-1-139-48954-6
  3. Zbigniew R. Dmochowski (1990). An Introduction to Nigerian Traditional Architecture: South-Eastern Nigeria, the Igbo- speaking Areas . Ethnographica Limited. ISBN 978-0-905788-28-9
  4. "Chief Okoroji's House, Arochukwu" . www.zodml.org . Retrieved 1 September 2016.