Georgie Badiel Liberty (an haife ta a ranar 7 ga watan Fabrairu, 1985) 'yar fafutuka da ke zaune da aiki a birnin New York. [1] Badiel ta kasance Miss Burkina Faso a shekarar 2003 da Miss Africa 2004.

Georgie Badiel
Rayuwa
Haihuwa 1988 (35/36 shekaru)
ƙasa Burkina Faso
Sana'a
Sana'a model (en) Fassara da marubuci

Tarihin Rayuwa gyara sashe

Ita ma marubuciya ce kuma mai fafutuka da ta ɗauki nauyin matsalar rashin ruwan sha a ƙasarta ta yammacin Afirka. A cikin ta ne ke tafiyar da gidauniyar Georgie Badiel wacce ta sadaukar da kanta wajen tara kuɗaɗe don tallafawa harkar. [2] Yanzu tare da marubucin littafin yara, Peter H. Reynolds da Susan Verde, ta haɗa littafin The Water Princess, littafin hoto wanda ke ba da labari game da matsananciyar buƙatar al'ummarta ta Afirka ta Yamma na neman ruwa a cikin rayuwarta tana yarinya wacce take mafarkin kawowa mutanenta ruwa mai tsafta. Penguin Random House ne ya buga littafin a cikin shekarar 2016. [3] [4]

Rayuwa ta sirri gyara sashe

Badiel ta auri Chid Liberty.

Karramawa da nasarori gyara sashe

An karrama ta da Chevalier Of Merit Burkinabe a ranar 28 ga watan Fabrairu a ofishin Burkina Faso a New York.

Manazarta gyara sashe

  1. "Georgie Badiel - Fashion Model - Profile on New York Magazine". nymag.com. Retrieved July 17, 2016.
  2. "Georgie Badiel Foundation - Activist". georgiebadielfoundation.org. July 23, 2015. Retrieved July 17, 2016.
  3. "'The Water Princess' Relates Childhood of Burkina Faso-Born Model Georgie Badiel". publishersweekly.com. Retrieved July 17, 2016.
  4. "The Water Princess by Susan Verde, Georgie Badiel - PenguinRandomHouse.com". Retrieved August 23, 2016.