Garuba suna ne na namiji musamman mutanen Najeriya da Nijar da aka bayar da suna da kuma sunan kaka da aka fi amfani da shi a tsakanin Musulmi, musamman a cikin al'ummar Hausawa . Garuba ko Garba daga harshen Larabci ne “al-garb” ma’ana sahabin annabi Muhammad, an binne Abubakar a gefen kudu da kabarin annabi. [1] Wannan suna Garuba/Garba a ko da yaushe ana danganta shi da duk mai suna Abu bakr ko Abubakar.

Garuba

Fitattun mutane masu suna

gyara sashe
  • Chris Abutu Garuba (1948), gwamnan sojan Najeriya.
  • Usman Garuba (an haife shi a shekara ta 2002), ɗan wasan ƙwallon kwando na ƙasar Sipaniya ɗan Najeriya.
  • Harry Garuba (1958 - 2020), haifaffen Najeriya marubucin wakoki kuma farfesa.
  1. "Name Search - Behind the Name". www.behindthename.com. Retrieved 2024-10-18.