Garkuwa da Mutane a Jami'ar Greenfield
Garkuwa da mutane a Jami'ar Greenfield, ya faru ne a ranar 20 ga watan Afrilun shekara ta 2021, lokacin da aka sace aƙalla ɗalibai da ma'aikata guda 23 a ƙauyen Kasarami, da ke karamar Hukumar Chikun, a Jihar Kaduna, Nijeriya. Yayin wani hari da wasu da ake zargin 'yan fashi da makami ne suka kai a Jami'ar Greenfield . Wannan shi ne karo na hudu da ake satar mutane daga wata makarantar ilimi a shekara ta 2021, kuma na biyar kenan tun daga watan Disambar shekara ta 2020, wanda ke zuwa makonni biyar da kwanaki shida bayan sace Afaka, inda aka sace dalibai guda 39.
Iri | aukuwa |
---|---|
Bayan Fage
gyara sasheHarin ya faru ne da karfe 8:15 na dare agogon yankin a ranar 20 ga watan Afrilun shekara ta 2021 a Jami'ar Greenfield . Hukumomin ‘yan sanda sun tabbatar da satar kuma sun ce wadanda ake zargin’ yan fashi da makami ne suka kutsa kai cikin makarantar suka yi awon gaba da daliban, yayin da suka kashe wani ma’aikaci guda. Masu garkuwan sun nemi fan miliyan 800 na fansa.
Kisa
gyara sasheA ranar 23 ga watan Afrilun shekara ta 2021, masu garkuwar sun kashe dalibai uku a hannunsu. An gano gawarwakin daliban da suka mutu a kauyen Kwanan Bature, wani wuri kusa da jami’ar. [1][2]
A ranar 26 ga watan Afrilun shekara ta 2021, an kashe wasu daliban jami'ar da aka sace.[3][4]
Duba kuma
gyara sashe- Satar Mutane a Najeriya
- Afaka satar mutane
- Kagara satar mutane
- Kankara satar mutane
- Makurdi satar mutane
- Satar Zamfara
Manazarta
gyara sashe- ↑ HassanWuyo, Ibrahim (23 April 2021). "Bandits kill 3 abducted Greenfield university students ― Kaduna govt". Vanguard Newspaper. Retrieved 24 April 2021.
- ↑ "Three students abducted from Nigeria university found shot dead". Al Jazeera. 23 April 2021. Retrieved 24 April 2021.
- ↑ HassanWuyo, Ibrahim (26 April 2021). "BREAKING: Two more Greenfield University students killed in Kaduna". Vanguard Newspaper. Retrieved 26 April 2021.
- ↑ "BREAKING: Bandits Kill Two More Abducted Greenfield University Students". Channels TV. 26 April 2021. Retrieved 26 April 2021.