Garba Ja Abdulqadir (An haife shi a shekarar alif dubu daya da dari tara da talatin da uku 1933) , a Katsina, Najeriya, ya riƙe muhimman mukamai da dama wanda suka hada da babban commisionan zabe na arewa. Minista Sakatare na noma a watan Augustan shekarar 1993. Gwmanatin Tarayya ta bashi lambar yabo na Sarkin Sudan,[1] sannan ya samu digir na digirgir daga jami’ar Usman Danfodiyo, kuma shine shugaban Jami’ar Lagos. Shi ne chiyaman na kamfanin John Holt Group da kuma sauran kamfanoni guda shida.[2][3]Akwai unguwa mai zaman kanta (Garba Ja Abdulkadir Crescent)[4] da aka sanya sunan a maimakonsa.

Kuruciya da Ilimi

gyara sashe

An haife Garba a 1933 kuma ya fara karatunsa daga 1944 zuwa 1947, daga bisani kuma a Govenrment College da ke Kaduna a tsakanin 1947-1950,sai kuma jami’ar Ibadan daga 1956 zuwa 1959 inda ya kammala karatunsa a fannin tarihi watau (BA History).[2]

Garba ya fara aiki a matsayin malami sannan daga baya ya koma Gwamnatin Yankin Arewacin Najeriya a matsayin mai gudanarwa. Ya zamo jami’in yanki (Divisional Officer) a Hadeja daga 1959 zuwa 1960, daga 1959 zuwa 1962 yana aiki da firimiya na Arewacin Najeriya a kaduna, sannan daga baya anyi mai canjin aiki zuwa ofishin Gwamna a matsayin sakatare na kusa a tsakanin 1961 zuwa 1962. Garba ya zamo mai gudanarwa na yankin babban birnin Kaduna 1965, sannan kuma ya zamo sakataren gundumar Plateau daga 1967 zuwa 1975.

A lokacin da aka kafa jihohi a Najeriya, Garba ya zamo sakatare na farko na gwamnatin mulkin soja na gwamnatin arewa ta tsakiya, daga bisani kuma yankin gundumar Kasuna, Zaria da Katsina (jihohin Katsina da Kaduna a yau) inda yayi aiki daga 1967 zuwa 1975 sannan ya ajiye aiki bayan shekaru takwas. Ya rike matsayin shugaban jami’oi kamar haka;

  • Jami'ar Lagos
  • Jami'ar Maiduguri
  • Jami'ar Usman Danfodiyo

Garba yayi aiki a majalisar kasa a tsakanin 1979 zuwa 1999, sannan ya rike matsayin chiyaman a wadannan wurare kamar haka;

  • National freight company
  • Nigerian Railway corporation
  • John holt Plc
  • Granges company
  • Hikima trading company
  • Kado farms

An naɗa shi cikin kwamitin amintattu na gidauniyar jihar Katsina, ya rike matsayin Minista Sakatare na noma a watan Augustan 1993. Gwmanatin Tarayya ta bashi lambar yabo na Sarkin Sudan, sannan ya samu digir na digirgir daga jami’ar Usman Danfodiyo da kuma jami’ar Lagos.

Manazarta

gyara sashe
  1. A Karofi, Hassan (October 23, 2001). "Sudan: Ja Abdulakadir Turbaned Sarkin Sudan". AllAfrica. Retrieved May 30, 2022.
  2. 2.0 2.1 Admin (2016-07-11). "ABDULKADIR, GARBA J.A. (OFR)". Biographical Legacy and Research Foundation. Retrieved 2022-05-29.
  3. Alessandro, Del Sole, (2010). Visual Basic 2010 unleashed. Sams, Pub. ISBN 978-0-672-33100-8. OCLC 874922564.
  4. "Garba Ja Abdulkadir Crescent - Real Estate Market Research and Data Nigeria and Africa - ei - Estate Intel". estateintel.com. Retrieved 2022-05-30.