Ganiyu Oboh, Farfesan Najeriya ne a fannin ilimin kimiyyar halittu da harhaɗa magunguna a Jami'ar Fasaha ta Tarayya ta Akure. A halin yanzu shi ne shugaban Sashin ɗakin gwaje-gwaje na Abinci da Nutraceutical a Sashen Biochemistry kuma ya ba da shawarar magani ga ciwon sukari.[1] A cikin shekarar 2021, an ba shi lambar yabo ta mafi kyawun bincike bisa ga Alper-Doger Scientific Index.[2]

Ganiyu Oboh
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a researcher (en) Fassara da biochemist (en) Fassara
Kyaututtuka
Mamba Makarantar Kimiyya ta Najeriya

Ganiyu Oboh ya samu digirin sa na farko a Jami’ar Tarayya ta Fasaha ta Akure, Sashen Biochemistry a shekarar 1992, Masters Technology da Digiri na uku a fannin Biochemistry a shekarun 1997 da 2002 a jami’a guda.[2] Ya yi karatun digirinsa na digiri a fannin ilimin kimiyyar halittu a cikin shekarar 2005 a Jami'ar Federal de Santa Maria, Santa Maria RS, Brazil da samun horon digiri na biyu a fannin Biochemistry da Toxicology tsakanin shekarun 2007 da 2008 a Technische Universität Dresden, Jamus.[2]

Manazarta

gyara sashe
  1. "FUTA scientist identifies nutritional causes, cures for diabetes". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2017-04-13. Archived from the original on 2021-12-14. Retrieved 2021-12-14.
  2. 2.0 2.1 2.2 Premium, Times (3 September 2021). "FUTA don ranked 'Nigerian best researcher'". Premiumtimes.