Mohamed Fouad Shafiq, Wanda aka fi sani da sunansa Fouad Shafiq ko Fouad Shafik (1899-1964) ɗan wasan Masar ne.[1]

Fu'ad Shafiq
Rayuwa
Haihuwa Kairo, 13 Oktoba 1899
ƙasa Misra
Harshen uwa Egyptian Arabic (en) Fassara
Mutuwa 2 Satumba 1964
Karatu
Harsuna Larabci
Egyptian Arabic (en) Fassara
Sana'a
Sana'a jarumi
IMDb nm0149565
kasar misra

Rayuwar farko

gyara sashe

An haifi Shafiq "Mohamed Fouad Shafiq" a ranar 13 ga watan Oktoba 1899, a Alkahira, Masar.[1] Mahaifinsa Bamasare ne ɗan asalin Turkiyya wanda danginsa suka isa Masar daga Karita; ɗan uwansa shi ne shahararren ɗan wasan kwaikwayo Hussein Riad.[2] Bayan rasuwar mahaifinsa Shafiq ya bar sakandirensa ya koma ƙasar Sudan inda ya yi aiki sannan kuma ya yi aure.

Aiki sana'a

gyara sashe

Bayan ya koma ƙasar Masar a shekarar 1924, Shafiq ya haɗu da Youssef Wahbi inda ya fara aikinsa a fim ɗin "Anthem of Hope". Bayan haka, ya kuma yi aiki a cikin wasan kwaikwayo da yawa a cikin ƙungiyar Fatima Rushdi. Ayyukansa sun bambanta tsakanin wasan ban dariya da ban tsoro.[1]

Ya mutu a ranar 2 ga watan Satumba, 1964.

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 1.2 (فؤاد شفيق (1899 - 1964)), El Cinema, retrieved 25 September 2017
  2. (حسين رياض (1897 - 1965), El Cinema, retrieved 25 September 2017, ولد (حسين محمود شفيق) في حي السيدة زينب بالقاهرة لأم سوريّة وأب مصري ميسور الحال يعمل بتجارة الجلود، وهو سليل أسرة تركية ترجع أصولها لحكام جزيرة (كريت).