Fred Agbedi
Frederick Yeitiemone Agbedi (An haife shi a ranar 20 ga a shekarar watan Febrariru, 1960).Ya kasance mai ilimantarwa ne, kuma dan siyasa daga jihar Bayelsa. Yana ɗaya daga cikin jiga-jigan da suka kirkiro jihar Bayelsa. Yana daga cikin kungiya mai karfi na yaren Ijo wanda suka sa aka kirkiri jihohi sabbi a Najeriya.[1]
Fred Agbedi | |||||
---|---|---|---|---|---|
11 ga Yuni, 2019 - District: Sagbama/Ekeremor
ga Yuni, 2015 - | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | 20 ga Faburairu, 1960 (64 shekaru) | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||
Imani | |||||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Farkon rayuwa da llimi
gyara sasheAn haifeshi a Aghoro, alkarya ne dake kusa da ruwa a karamar hukumar Ekeremor, a jihar Bayelsa. Ya halarci makarantar jihar Aghoro da 'Oproza Grammar School' Patani don karatunsa na Firamare da Sakandare. Ya mallaki ilimin NCE da kwarewa akan Turanci da Tarihi daga kwalejin Ilimi na Warri, jihar Delta. Har wa yau ya mallaki digiri na ilimi (B. Ed) a Turanci daga Jami'ar Patakwal (University of Port Harcourt kuma yayi mastas dinshi a Public Administration a Jami'ar Abuja.[2]
Siyasa
gyara sasheAbedi ya zama cikakken dan siyasa a shekarar 1992 bayan ya shiga jam'iyyar (NRC) kuma ya zama sakataren ƙungiyar a kauyensu na Ekeremor.