Muhammad Fawzi Mahjoub Al-Mardi (1953 - 5 May 2023), kuma aka sani da Fozi el-Mardi ( Larabci: فوزي المرضي‎ ), ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan ƙasar Sudan, koci, kuma mai gudanarwa. Ya buga wasa a kungiyar Al-Hilal FC a shekarar 1971, kuma ya buga wasanni 29 na kasa da kasa a kungiyar kwallon kafa ta Sudan . [1] [2] Ya lashe gasar Premier ta Sudan a shekarar 1973 da kuma kofin Sudan a 1977.

Fozi el-Taris
Rayuwa
Haihuwa 1953
Mutuwa 5 Mayu 2023
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa da association football coach (en) Fassara

Al-Mardi ya yi ritaya daga buga kwallo a shekara ta 1980, inda ya fara aiki a fagen horo tun 1982 a kungiyoyin wasanni da dama a Sudan. [3] Daga baya ya zama memba na kwamitin gudanarwa na kungiyar Al-Hilal FC. [4] [5]

A ranar 5 ga Mayu, 2023, a Asibitin Al Nou da ke Omdurman, Al-Mardi ya mutu kwanaki bayan mutuwar 'yarsa, Alaa wacce wani makami ya same ta a ranar 17 ga Afrilu, kwanaki 2 daga farkon rikicin Sudan na 2023 . Har ila yau matarsa, Zeinat Ahmed Othman, ta samu rauni sakamakon harbin bindiga. [6] [7]

Manazarta gyara sashe

  1. name=":1">السودان, نبض (2023-05-06). "وفاة كابتن الهلال الاسبق ومدربه فوزي المرضي بعد أيام قليلة من وفاة إبنته". صحافة العرب (in Larabci). Retrieved 2023-08-19.
  2. Strack-Zimmermann, Benjamin. "Fawzi El-Mardi (Player)". www.national-football-teams.com (in Turanci). Retrieved 2024-03-14.
  3. "عاجل.. وفاة كابتن الهلال السابق ومدربه فوزي المرضي بعد أيام قليلة من وفاة إبنته دكتورة آلاء بطلقة طائشة - النيلين" (in Larabci). 2023-05-05. Retrieved 2023-08-19.
  4. "فوزي المرضي: تسجيلاتنا ستعتمد على الرديف واللاعبين الشباب - النيلين" (in Larabci). 2015-10-31. Retrieved 2023-08-19.
  5. السودان, نبض (2023-05-06). "وفاة كابتن الهلال الاسبق ومدربه فوزي المرضي بعد أيام قليلة من وفاة إبنته". صحافة العرب (in Larabci). Retrieved 2023-08-19.السودان, نبض (2023-05-06).
  6. name=":0">"عاجل.. وفاة كابتن الهلال السابق ومدربه فوزي المرضي بعد أيام قليلة من وفاة إبنته دكتورة آلاء بطلقة طائشة - النيلين" (in Larabci). 2023-05-05. Retrieved 2023-08-19."عاجل.. وفاة كابتن الهلال السابق ومدربه فوزي المرضي بعد أيام قليلة من وفاة إبنته دكتورة آلاء بطلقة طائشة - النيلين" (in Arabic).
  7. "رصاصة اخترقت قلبها داخل منزلها.. مقتل ابنة كابتن فريق الهلال السوداني". Al-Arabiya. 2023-04-19.