Flavia Oketch (an haife ta a ranar 16 ga watan Yuli shekara ta 1986) 'yar wasan Ƙwallan kwando ce ' yar Uganda, wacce ke taka leda a ƙungiyar ƙwallon kwando ta mata ta Uganda . [1]

Flavia Oketcho
Rayuwa
Haihuwa Kampala, 16 ga Yuli, 1986 (38 shekaru)
ƙasa Uganda
Karatu
Makaranta Makarantar Sakandare ta Kitante Hill
Makarantar Kwalejin Makerere
Jami'ar Kirista ta Uganda
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a basketball player (en) Fassara
Itinerary
Ƙungiyoyi Shekaru Pos Nbr
Jami'ar Kirista ta Uganda-
 

Tarihi da ilimi

gyara sashe

An haife ta a yankin tsakiyar Uganda a ranar 16 ga Yuli 1986 kuma ta girma a can.

A 1992, Oketch ta shiga makarantar firamare ta Nakasero amma daga baya ta koma Kitante Primary School, inda ta yi karatu daga 1993 zuwa 1998. [2]

A cikin 1999–2002, ta halarci Makarantar Sakandare ta Kitante Hill don ilimin matakin O'. a cikin 2001, yayin da take Kitante Hill, ta buga wasanta na farko tare da Lady Bucks. A cikin 2003–2004, ta shiga Makarantar Koleji ta Makerere don S5 amma daga baya ta shiga makarantar sakandare ta Najja inda ta yi jarrabawar A'level. [2]

Oketch ya halarci Jami'ar Kirista ta Uganda a 2007 don yin digiri a Mass Communications. A cikin 2008 ta taimaka wa ƙungiyar ƙwallon kwando ta UCU, Lady Cannons, don lashe taken gasar kuma an ba ta MVP .

Sana'a da kyaututtuka

gyara sashe

Ta buga wasanta na farko a gasar a 2001 tare da Lady Bucks. A shekara ta 2004 an zabe ta MVP a gasar zakarun kulob na Gabashin Afrika, [2] wanda ta taimaka wajen lashe kofunan lig biyu.

a 2005, ta wakilci Uganda a gasar Zone V Nations Tournament.

Manazarta

gyara sashe
  1. "Flavia OKETCHO at the FIBA Women's Afrobasket 2017". FIBA.basketball (in Turanci). Retrieved 2020-04-07.
  2. 2.0 2.1 2.2 "Oketcho dribbles family, motherhood and hoops". Daily Monitor (in Turanci). Retrieved 2020-04-07.