Filin jirgin sama
Filin jirgin sama wuri ne na musamman da aka samar masa da na'urori na zamani da ma'aikata domin sauka tare da tashin jiragen sama.
![]() | |
---|---|
![]() | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na |
aerodrome (en) ![]() ![]() ![]() |
Has quality (en) ![]() |
airport security (en) ![]() |
Filin jirigin sama ya kunshi abubawa da dama wadanda ake bukata na musamman domin samar da cikakkun tsaro, kulawa, walwala, samar da cikakkun na'urorin zamani da samar da bayanai wadanda suka shafi kula da tashi da kuma saukan jiragen saman. Yana daya daga cikin abubuwan da aka samar wa filin jirgin sune dogon titi wanda zai wadaci jirgi yayi gudun mai nisa wanda zai taimaka masa wurin tashi sama da kuma sauka kasa, wadataccen filin ajiye jiragen sama.
Manyan filayen jiragen musamman na kasa da kasa, sunada wurare na musamman inda jami'an custom da na immigration ke kula da shige da ficen matafiya. Haka kuma ana samun gidajen sayar da abinci, bankuna da kuma manyan kantuna na zamani duk a cikin su.