Fidelis Okoro

Dan siyasar Najeriya

Fidelis C. Okoro ɗan siyasar Najeriya ne wanda kuma ya kasance Sanata mai wakiltar Enugu ta Arewa Sanatan jihar Enugu a farkon jamhuriya ta huɗu ta Najeriya, wanda ya yi takara a jam'iyyar Alliance for Democracy (AD). Ya kuma fara aiki a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 1999.[1]

Fidelis Okoro
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

3 ga Yuni, 2003 - 5 ga Yuni, 2007 - Ayogu Eze
District: Enugu North
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

29 Mayu 1999 - 29 Mayu 2007 - Ayogu Eze
District: Enugu North
Rayuwa
Haihuwa Jihar Enugu
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party
Alliance for Democracy (en) Fassara

Bayan ya hau kan kujerar sa a majalisar dattawa a watan Yunin shekarata 1999, Okoro ya zama kwamitocin kula da ayyukan majalisar dattawa, masana’antu (shugaban ƙasa), harkokin ƴan sanda, noma da kuma Neja Delta.[2] Ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar People's Democratic Party (PDP) kuma ya zama abokin Gwamna Chimaroke Nnamani.[3] A cikin watan Disambar 2001, Cif Mike Ejinima, mai neman zama gwamna, ya shigar da ƙarar sa a gaban kotu tare da Nnamani, Ike Ekweremadu da David Atigwe, ɗan majalisar dokokin jihar Enugu.[4] An sake zaɓen shi a cikin watan Afrilun 2003 akan tikitin PDP.[5]

Manazarta gyara sashe