Fermín López
Fermín López Marín[1] (an haife shi ranar 11 ga watan Mayu,Shekara ta 2003) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Sipaniya wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta FC Barcelona Atlètic.[2][3]
Fermín López | |||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | El Campillo (en) , 11 Mayu 2003 (21 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Ispaniya | ||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||
Harsuna |
Yaren Sifen Catalan (en) | ||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Mai buga tsakiya | ||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 176 cm | ||||||||||||||||||||||||||
IMDb | nm15100632 |
Fermín ya fara buga kwallon kafa tare da kungiyar din El Campillo na gida,[4] kuma ya bi shi tare da zama a Recreativo Huelva kafin ya koma kungiayr Real Betis a shekarar ta 2012.A lokacin rani na shekarar ta 2016 ne, ya koma makarantar matasa na kungiyar kwallon kafan Barcelona. A ranar 19 ga watan Agusta a shekarata 2022 ne, ya sanya hannu kan kwangilar ƙwararru tare da kungiyar Barcelona Atlètic na tsawon shekaru biyu har zuwa shekarar 2024, kuma nan da nan ya tafi rance tare da Linares Deportivo a cikin Primera Federación na kakar 2022-23. Bayan da ya yi aiki mai karfi a horo tare da kungiyar Barcelona kafin preseason, an kira shi zuwa ga manyan 'yan wasan preseason a watan Yulin shekarar 2023. Ya sami karɓuwa na kasa da kasa bayan da ya yi rawar gani ga kungiyar tasa ta Barcelona a wasan sada zumunta da suka ci 3-0 a kan abokan hamayyarsu Real Madrid. Wanda aka buga a ranar 29 ga watan Yuli a shekarata 2023. Bayan wasan, Xavi ya tabbatar da cewa Fermín zai ci gaba da zama tare da babbar kungiyarsu don kakar 2023-24.
Tsarin Wasanshi
gyara sasheFermín ɗan wasan tsakiya ne mai kuzari, mai ƙafar ƙafar hagu, wanda kuma yana da damar itama a fagen taka leda sannan ya kasance matsayin ɗan wasan tsakiya mai kai hari da winger. Ya ƙware a fasaha, yana da matuƙar motsi daga ƙwallon, ƙware wajen yin amfani da sararin samaniya, kuma yana da ƙwazo da maƙasudi da taimako.
Hotuna
gyara sasheManazarta
gyara sashe- ↑ https://www.goal.com/en-ng/lists/fermin-lopez-barcelona-young-star-whole-package/blt848b823ea7cad891
- ↑ https://www.fcbarcelona.com/en/football/first-team/news/3610338/fermin-lopez-explodes-onto-the-clasico-stage
- ↑ https://www.football-espana.net/2023/07/30/who-is-fermin-lopez-barcelonas-20-year-old-el-clasico-sensation
- ↑ https://www.forbes.com/sites/tomsanderson/2023/07/30/newest-fc-barcelona-star-fermin-lopez-could-leave-club-for-free-after-stunning-cameo-in-el-clasico/?sh=24ab205e2e4e