Feo-Gasy
Feo-Gasy wasu makaɗa ne daga Madagascar da ke yin kade-kade na gargajiyar ba-gasy na mutanen Merina na tsaunukan tsakiyar tsaunukan da ke kusa da babban birnin kasar Antananarivo. An kafa ƙungiyar a cikin shekarar 1994 ta fitaccen ɗan wasan guitar Erick Manana [1] kuma ya fito har zuwa mutuwarsa a shekarar 2001 fitaccen ɗan wasan sodina Rakoto Frah, shi ne kaɗai mawaƙin Malagasy da aka taɓa nunawa akan kuɗin gida (Local currency). Ƙungiyar ta samo asali ne daga mawaƙa da makaɗa Erick Manana, dan wasan sodina da mawaƙi Rakoto Frah, mawaƙi da guitarist Jean-Colbert Ranaivoarison ("Rakôly"), mawaƙi Famantsoa Rajaonarison ("Fafa") da François-Daniel Rabeanirainy (" Beny"), da ɗan wasan valiha Bariliva Rasoavatsara, wanda ya mutu a cikin watan Disamba 2012.[2]
Feo-Gasy | |
---|---|
musical group (en) | |
Bayanai | |
Work period (start) (en) | 1994 |
Hotuna
gyara sasheTake | An sake shi | Lakabi | Waƙoƙi (Tsawon) |
---|---|---|---|
Ramano | 2000 | Daqi | 12 (43'55) |
Tsofy Rano | 1996 | Mélodie | 12 (43'55) |
Duba kuma
gyara sashe- Music of Madagascar