Felix Olorunfemi
Felix Olorunfemi (an haife shi takwas 8 ga watan Yuni, a shekara ta 1966) shi ne Bishop na Anglican na Etsako [1] a Lardin Bendel [2] na Cocin Najeriya .
An tsarkake shi a matsayin Bishop na biyu ne na Etsako a Lokoja a watan Maris na dubu biyu da ashirin 2020. [3]
Ya kasance Archdeacon na Agbor-Obi Archdeaconry (wata majami'a ko kuma coci na musamman) a cikin diocese na Ika .
An haifi Olorunfemi a ranar takwas 8 ga Yuni alif dari tara da sittin da shida 1966 a Okpella, Etsako, Jihar Edo, inda ya tafi makarantar firamare sannan Ikpomaza Grammar School da Kwalejinmu ta Lady of Fatima, Auchi. [ana buƙatar hujja][<span title="This claim needs references to reliable sources. (January 2023)">citation needed</span>]
Ya kammala karatu a Jami'ar Jihar Bendel da Kwalejin tauhidin Ezekiel, Ekpoma, tare da difloma a tauhidi a shekara ta dubu biyu da biyar 2005. [ana buƙatar hujja][<span title="This claim needs references to reliable sources. (January 2023)">citation needed</span>]
Olorunfemi ya koyar da Turanci a makarantar Mary da Martha Juniorate Convent, Igbodo, daga shekarar dubu biyu da biyu 2002 zuwa 2007 a ƙarƙashin Shugaban lokacin, Godfrey Ifeanyichukwu Ekpenisi . [4]
Bayanan da aka ambata
gyara sashe- ↑ Office, Anglican Communion. "Anglican Communion: Diocese". Anglican Communion Website.
- ↑ "Ecclesiastical Province of Bendel | Church of Nigeria (Anglican Communion)" (in Turanci). 26 March 2020. Retrieved 2021-03-10.
- ↑ "RT REVD FELIX OLORUNFEMI ENJOINS CHRISTIANS NOT TO GIVE UP IN DIFFICULT TIMES | Church of Nigeria (Anglican Communion)" (in Turanci). 2020-06-10. Retrieved 2021-03-10.
- ↑ adminacnn. "Church of Nigeria Elect The Ven. Felix Unuokhe Olorunfemi For Estako Diocese | Advent Cable Network Nigeria" (in Turanci). Retrieved 2021-03-10.