Federal College of Education (Technical), Potiskum
Kwalejin Ilimi ta Tarayya (Reshen Fasaha), Potiskum babbar makarantar gwamnatin tarayya ce da ke garin Potiskum, Jahar Yobe, a Najeriya. Da fari an kawo mata reshen jami’ar Fasaha ta Tarayya ta Minna kafin daga bisa ni aka ɗauke ta tare da maye gurbin ta da Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, (ATBU) Bauchi don karatun digiri. Kwalejin ta fara samar da shirye-shiryen karatun PGDE a cikin shekarar 2021. Shugaban Kwalejin na yanzu shi ne Dr. Muhammad Madu Yunusa. [1]
Federal College of Education (Technical), Potiskum | |
---|---|
| |
Learning Re-defined | |
Bayanai | |
Iri | college (en) |
Ƙasa | Najeriya |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 1991 |
fcetpotiskum.edu.ng |
Tarihi
gyara sasheAn kafa Kwalejin Ilimi ta Tarayya (Reshen Fasaha) da ke cikin garin Potiskum ne a shekarar 1991. Inda tun asali da fari a na kiranta ne da suna Federal Advanced Teachers' College (FATC), Yola.
Tsangayoyi
gyara sasheKwalejin tana da tsangayu kamar haka waɗanda a ƙarƙashinsu akwai sassa daban-daban.
- Tsangayar Ilimin Kimiyya
- Tsangayar Ilimin Fasaha
- Tsangayar Ilimin Kasuwanci
- Tsangayar Ilimin Sana'a
- Tsangayar Ilimi
Sassa/Rukunai
gyara sasheTsangayar Ilimin Kimiyya
- Ginin Sashen Kimiyyar Sinadarai
- Ginin Sashen Kimiyyar Makamashi
- Ginin Sashen Kimiyyar Lissafi
- Ginin Sashen Kimiyyar Halittu
- Ginin Sashen Hadakar Kimiyya
Tsangayar Ilimin Sana'a
- Ginin Sashen Kimiyyar Noma
- Ginin Sashen Kimiyyar Tattalin Gida
- Ginin Sashen Kimiyyar Zane-Zane
Tsangayar Ilimin Fasaha
- Ginin Sashen Rukunin Lantarki
- Ginin Sashen Gyaran Mota
- Ginin Sashen Gine-Gine
- Ginin Sashen Kayan Aikin Katako
- Ginin Sashen Kira
Tsangayar Ilimin Kasuwanci
- Ginin Sashen Rukunin Sakateriya
- Ginin Sashen Rukunin Akawunta
Tsangayar Ilimi
- Rukunin Ilimin Firamare
- Rukunin Ilimin Yara a Matakin Farko
Darussa
gyara sasheCibiyar tana ba da darussa kamar haka;
- Ilimi da Physics
- Ilimin Fasahar Gini
- Ilimin Fasaha na Aikin Katako
- Hadin gwiwar Kimiyya da Makamashi
- Ilimin Lissafi
- Ilimin Tattalin Gida/Girke-Girke
- Ilimin Kwamfuta da Sinadarai
- Ilimin Sinadarai/Hadaddiyar Kimiyya
- Ilimin Kwamfuta/Makamashi
- Ilimin Lantarki/Kayan Wuta
- Ilimin Fasahar Gyaran Mota
- Ilimin Halittu da Hadaddiyar Kimiyya
- Ilimin Kimiyyar Noma
- Ilimin Kasuwanci
- Ilimin Kwamfuta da Nazarin Halittu
- Ilimin Kimiyyar Kwamfuta da Lissafi
- Kimiyyar Noma
- Ilimin Kula da Yara a Matakin Farko
- Ilimin Fasaha
- Ilimin Fasahar Zane
- Karatun Ilimin Firamare
- Ilimin Fasahar Ƙarfe
Alaka/Reshe
gyara sasheCibiyar tana da alaƙa/reshe da Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa don bayar da karatun da zai kai ga samun shaidar karatun digiri na fannin ilimi, (B.Ed.) a wadannan bangarorin;
- Ilimin Lissafi
- Ilimin Fasahar Aikin Karfe
- Ilimin Nazarin Halittu
- Ilimin Aikin Katako
- Ilimin Fasahar Mota
- Ilimin Lantarki/Kayan Wuta
- Ilimin Sinadarai
- Ilimin Kimiyyar Kwamfuta
- Ilimin Makamashi
- Ilimin Gine-Gine
- Ilimin Kimiyyar Noma
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-12-14. Retrieved 2021-12-14.