Faustine Fotso
Honourable Faustine Villanneau Chebou Kamdem Fotso, an haife ta a ranar 12 ga watan Yuni, a shekara ta alif 1965, masaniyar kimiyyar kwamfuta ce, masaniyar muhalli, kuma lauya daga ƙasar Kamaru .
Faustine Fotso | |||
---|---|---|---|
District: West (en) | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | 12 ga Yuni, 1965 (59 shekaru) | ||
ƙasa | Kameru | ||
Sana'a | |||
Sana'a | computer scientist (en) , Lauya da environmentalist (en) | ||
Wurin aiki | Baham (en) | ||
Mamba | Q122418360 | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | Cameroon People's Democratic Movement (en) |
Rayuwar jama'a
gyara sasheA cikin shekarar 2012, Fotso ta kasance mataimakiyar magajin garin Baham na 1, wani gari a yammacin Kamaru. A cikin shekarar 2013, an zaɓe ta a matsayin 'yar majalisa a Majalisar Dokoki ta ƙasa, mai wakiltar tsaunukan Yammacin Turai. [1] Ta zauna a Kwamitin Dokokin Tsarin Mulki kuma tana cikin Jam'iyyar Dimokuraɗiyya ta Jama'ar Kamaru .[2]
Ayyukan ilimi
gyara sasheFotso ta rubuta littafin "Nazarin Tasirin Muhalli a Faransanci da Dokokin Kamaru" a cikin shekarar 2009 a matsayin wani ɓangare na Shirin Masters na Dokar Ƙasa da Ƙasa da Muhalli a Jami'ar Limoges .[3]
Ayyukan sadaka
gyara sasheFotso ita ce ta kafa ƙungiyar agaji mai suna "Flame of Love, of Peace and Justice" wadda ta yi taron farko a ranar 20 ga watan Satumba, 2016.[4]
Kyauta
gyara sasheA ranar 20 ga watan Mayu, 2016, Fotso ta sami lambar yabo ta farar hula zuwa matsayi na jami'in oda a bikin ranar haɗin kan ƙasa karo na 44 a Baham.[5]
Iyali
gyara sasheFotso ta auri Lucas Fotso, darektan yanki na kamfanin lantarki na ƙasar Kamaru Aes Sonel Littoral.[6]Tare suna da yara biyar.
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Current Legislative Period : List of 180 members". www.assnat.cm (in Turanci). Retrieved 2018-03-08.[permanent dead link]
- ↑ "Cameroun: Hon Fotso Faustine - " Nous voulons parler le langage de la vérité à Baham "". allAfrica.fr (in Faransanci). Retrieved 2018-03-08.
- ↑ "Memoire Online - Etude d'impact environnemental en droit français et camerounais - Faustine Villannaeau FOTSO CHEBOU KAMDEM". Memoire Online. Retrieved 2018-03-08.
- ↑ NSANGOU, MAMA (3 October 2016). "Nous Voulons Faire Bloc Pour Les Causes Humaines".
- ↑ Cameroun, Actu (2016-05-26). "Cameroun, 20 Mai 2016 dans les Hauts-plateaux : Fotso Fostine en vedette en Baham :: CAMEROON". Actu Cameroun (in Faransanci). Retrieved 2018-03-08.
- ↑ "Energie électrique: un vaste réseau de fraude démantelé par Aes Sonel à Douala". fr.africatime.com (in Faransanci). Retrieved 2018-03-08.[permanent dead link]